Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Satumba 2027 › Satumba 15
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Satumba 15, 2027
Laraba · Mako na 24 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Laraba a mako na 24 na lokacin yau da kullum
Tunawa · Launin ibada: fari
Uwargidanmu ta Baƙin Ciki · Tunawa
Karatun yini
Karatu na farko
14Ko da yake ina sa zuciya zo wurinka nan ba da daɗewa ba, ina rubuta muka waɗannan umarnai domin, 15in na yi jinkiri, za ka san yadda ya kamata mutane su tafiyar da halayensu a cikin jama’ar Allah, wadda take ikkilisiyar Allah rayayye, ginshiƙi da kuma tushen gaskiya. 16Ba shakka, asirin addini da girma yake. Ya bayyana cikin jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, mala’iku suka gan shi, aka yi wa’azinsa cikin al’ummai, aka gaskata shi a duniya, aka ɗauke shi sama cikin ɗaukaka.
Zaburar amsawa
1Yabi Ubangiji. Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro. 2Ayyukan Ubangiji da girma suke; dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu. 3Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne, adalcinsa kuma zai dawwama har abada. 4Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa; Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma. 5Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa; yakan tuna da alkawarinsa har abada. 6Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa, yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai.
Bishara
ko: Luk 2:33–35
25To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin. 26Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Mace, ga ɗanki,” 27ga almajirin kuwa ya ce, “Ga mahaifiyarka.” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi