Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Satumba 2027 › Satumba 9

Kalandar Ortodoks · 27 ga Agusta (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Satumba 9, 2027

Alhamis · Mako na 12 bayan Fentekos · Sauti na 2

Bukukuwa da waliyyai

Venerable Pœmen the Great († c. 450)

Azumi

Babu azumi

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Wasiƙa

2Kor 7:1–10

1Da yake muna da waɗannan alkawura, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah. 2Ku saki zuciya da mu. Ba mu yi wa kowa laifi ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu cuci kowa ba. 3Ba na faɗin wannan don in sa muku laifi. Na riga na gaya muku yadda muke ƙaunarku ƙwarai cikin zukatanmu, har babu abin da zai iya raba ku da ƙaunarmu, ko a mutuwa ko a rayuwa. 4Na amince da ku gaya, ina kuma taƙama da ku ƙwarai. Na ƙarfafa sosai. Duk da wahalce wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske. 5Gama sa’ad da muka zo Makidoniya, jikin nan namu bai sami hutu ba, sai ma aka matsa mana a ta kowane gefe, a waje ga rikici, a zukatanmu kuma ga tsoro. 6Amma Allah, wanda yakan yi wa masu ɓacin rai ta’aziyya ya yi mana ta’aziyya da zuwan Titus, 7ba ma don zuwansa kaɗai ba, har ma a game da ƙarfafa zuciyan nan da ya samu a wurinku. Ya gaya mana yadda kuke so ku gan ni sosai, da kuma yadda kuka yi baƙin ciki game da abin da ya faru, da niyyar da kuka yi na goyon bayana. Wannan ne ya sa na ji daɗi ƙwarai. 8Ko da na ɓata muku rai ta wurin wasiƙata, ba na baƙin ciki da haka. Ko da yake dā kam na yi baƙin ciki, don na lura wasiƙata ta ɓata muku rai, amma na ɗan lokaci ne kawai. 9Duk da haka, yanzu ina farin ciki, ba don na sa ku baƙin ciki ba, sai dai domin baƙin cikinku ya kai ku ga tuba. Gama kun yi baƙin ciki kamar yadda Allah ya so, saboda haka, ba ku yi hasarar kome a sanadinmu ba. 10Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa.

Bishara

Mar 1:29–35

29Da suka bar majami’ar, sai suka tafi gidan su Siman da Andarawus, tare da Yaƙub da Yohanna. 30Surukar Siman tana kwance da zazzaɓi, sai suka gaya wa Yesu game da ita. 31Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya sāke ta, ta kuma yi musu hidima. 32A wannan yamma, bayan fāɗuwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu. 33Duk garin ya taru a ƙofar gidan. 34Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi. 35Da sassafe, tun da sauran duhu, Yesu ya tashi, ya bar gida, ya tafi wani wurin da ba kowa, a can ya yi addu’a.

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Agusta 27 a kalandar ikilisiya shi ne Satumba 9 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi