Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Agusta 2027 › Agusta 20

Kalandar Ortodoks · 7 ga Agusta (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Agusta 20, 2027

Juma’a · Mako na 9 bayan Fentekos · Sauti na 7

Bukukuwa da waliyyai

Afterfeast of the Transfiguration of the Lord

Azumin Barcin Uwar Allah

Azumi mai tsanani (busasshen abinci: burodi, ganye, ’ya’yan itace)

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Wasiƙa

1Kor 14:26–40

26Me za mu ce ke nan ’yan’uwa? Sa’ad da kuka taru, wani yakan yi waƙa, wani koyarwa, wani wahayi, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Dole ne a yi duka don gina ikkilisiya. 27In kuwa waɗansu za su yi magana a wani harshe, to, kada su fi mutum biyu ko uku, kuma a yi bi da bi, wani kuma yă fassara. 28In babu mai fassara, sai mai magana yă yi shiru a cikin ikkilisiya, yă yi wa kansa magana da kuma Allah. 29Annabawa biyu ko uku za su iya yin magana, sauran kuma sai su auna a hankali abin da aka faɗa. 30In kuma wahayi ya zo wa wani da yake zaune, sai mai magana na farko yă yi shiru. 31Dukanku kuna iya yin annabci bi da bi, domin kowa yă sami koyarwa da ƙarfafawa. 32Ruhohin annabawa kuwa suna ƙarƙashin sarrafawar annabawa. 33Gama Allah, ba Allah mai sa rikicewa ba ne, sai dai mai salama. Kamar yadda yake a dukan ikkilisiyoyi na tsarkaka. 34Ya kamata mata su zauna shiru a cikin ikkilisiyoyi. Ba su da izinin yin magana, sai dai su yi biyayya yadda Doka ta faɗi. 35In suna so su yi tambaya game da wani abu, ya kamata su tambayi mazansu a gida, domin abin kunya ne mace tă yi magana a cikin ikkilisiya. 36Shin, a kanku ne maganar Allah ta fara? Ko kuma a gare ku ne kaɗai ta iso? 37In wani yana tsammani shi annabi ne, ko yana da baiwar ruhaniya, bari yă gane cewa abin da nake rubuta muku umarnin Ubangiji ne. 38In ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi. 39Saboda haka ’yan’uwana, ku yi marmarin yin annabci, kada kuma ku hana magana da harsuna. 40Sai dai a yi kome daidai da kuma cikin tsari.

Bishara

Mat 21:12–14, 17–20

12Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai. 13Ya ce musu, “A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan addu’a,’ amma kuna mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ” 14Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su. 17Sai ya bar su, ya fita daga birnin ya tafi Betani, inda ya kwana. 18Kashegari da sassafe, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa cikin birni, sai ya ji yunwa. 19Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, “Kada ka ƙara yin ’ya’ya!” Nan da nan itacen ya yanƙwane. 20Sa’ad da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya itacen ɓauren ya yanƙwane nan da nan haka?”

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Agusta 7 a kalandar ikilisiya shi ne Agusta 20 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi