Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Agusta 2027 › Agusta 8

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Agusta 8, 2027

Lahadi · Mako na 19 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Lahadi ta 19 ta lokacin yau da kullum

Lahadi · Launin ibada: kore

Karatun yini

Karatu na farko

1Sar 19:4–8

4Shi kuma ya yi tafiya yini guda zuwa cikin hamada. Ya zo wurin wani itacen tsintsiya, ya zauna a ƙarƙashinsa, ya roƙa yă mutu. Ya ce, “Ya ishe ni haka, Ubangiji, ka ɗauki raina; ban fi kakannina ba.” 5Sa’an nan ya kwanta a ƙarƙashin itacen ya yi barci. Farat ɗaya sai wani mala’ika ya taɓa shi, ya ce, “Tashi ka ci abinci.” 6Ya duba kewaye, sai ga wainar burodi kusa da kansa a bisa garwashin wuta mai zafi, da kuma tulun ruwa. Ya ci, ya sha, sa’an nan ya sāke kwanta. 7Mala’ikan Ubangiji ya sāke dawowa sau na biyu ya taɓa shi, ya ce, “Tashi ka ci abinci, gama tafiyar za tă yi maka yawa.” 8Saboda haka ya tashi ya ci, ya kuma sha. Ta wurin ƙarfin da ya samu saboda wannan abinci, ya yi tafiya yini arba’in da dare arba’in, sai da ya kai Horeb, dutsen Allah.

Zaburar amsawa

Zab 34:1–8

1Ta Dawuda. Sa’ad da ya yi kamar ya haukace a gaban Abimelek, Wanda ya kore shi, ya kuwa tafi. Zan gode wa Ubangiji kullayaumi; yabonsa kullum za su kasance a leɓunana. 2Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji; bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki. 3Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni; bari mu ɗaukaka sunansa tare. 4Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro. 5Waɗanda suke dubansa sukan haskaka; fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya. 6Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi; ya cece shi daga dukan wahalarsa. 7Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa, ya kuwa cece su. 8Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau; mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.

Karatu na biyu

Afi 4:30–5:2

30Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa. 31Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. 32Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku. 5:1Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ’ya’ya, 2ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.

Bishara

Yoh 6:41–51

41Da jin haka, Yahudawa suka fara gunaguni a kansa, domin ya ce, “Ni ne burodin da ya sauka daga sama.” 42Suka ce, “Kai, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusuf, wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa duk mun san su? Yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko daga sama?’ ” 43Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ku daina gunaguni a junanku. 44Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe. 45A rubuce yake a cikin Annabawa cewa, ‘Allah zai koyar da dukansu.’ Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina. 46Ba wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda ya zo daga Allah; shi ne kaɗai ya taɓa ganin Uban. 47Gaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami. 48Ni ne burodin rai. 49Kakannin-kakanninku sun ci Manna a hamada, duk da haka suka mutu. 50Amma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba. 51Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.”

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi