Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Yuni 2027 › Yuni 8

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Yuni 8, 2027

Talata · Mako na 10 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Talata a mako na 10 na lokacin yau da kullum

Ranar mako · Launin ibada: kore

Karatun yini

Karatu na farko

2Kor 1:18–22

18Kamar dai yadda ba shakka Allah yake mai aminci, haka ma maganar da muka yi muku, ba “I” da kuma “A’a” ba ce. 19Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku wa’azinsa, ai, ba “I” da “A’a” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum. 20Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah. 21Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu, 22ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yă tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba.

Zaburar amsawa

Zab 119:129–133, 135

129Farillanka masu banmamaki ne; saboda haka nake yin biyayya da su. 130Fassarar maganganunka sukan ba da haske; sukan ba da ganewa ga marar ilimi. 131Ina hakkin da bakina a buɗe, ina marmarin umarnanka. 132Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai, yadda kullum ka yi wa waɗanda suke ƙaunar sunanka. 133Ka bi da sawuna bisa ga maganarka; kada ka bar zunubi yă mallake ni. 135Ka sa fuskarka ta haskaka a kan bawanka ka kuma koya mini ƙa’idodinka.

Bishara

Mat 5:13–16

13“Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka. 14“Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa. 15Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida. 16Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi