Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Mayu 2027 › Mayu 6
Kalandar Ortodoks · 23 ga Afirilu (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Mayu 6, 2027
Alhamis · Mako Mai Haske · Sauti na 5
Bukukuwa da waliyyai
Alhamis a Mako Mai Haske
Mako ba azumi
Babu azumi
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Addu’ar yamma: karatu (domin Waliyyi George)
9Dukan al’ummai su taru mutane kuma su tattaru. Wane ne a cikinsu ya yi faɗar wannan ya kuma yi mana shelar abubuwan da suka riga suka faru? Bari su kawo shaidunsu don su tabbatar cewa sun yi daidai, don waɗansu su ji su kuma ce, “Gaskiya ne.” 10“Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji, “bawana kuma wanda na zaɓa, saboda ka sani ka kuma gaskata ni ka kuma fahimci cewa ni ne shi. Kafin ni babu allahn da aka siffanta, ba kuwa za a yi wani a bayana ba. 11Ni kaɗai, ni ne Ubangiji, kuma in ban da ni babu wani mai ceto. 12Na bayyana na ceci na kuma furta, Ni ne, ba wani baƙon allah a cikinku. Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji, “cewa ni ne Allah. 13I, kuma tun fil azal ni ne shi. Babu wani da zai amshi daga hannuna. Sa’ad da na aikata, wa zai iya sauyawa?” 14Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, “Saboda ku zan aika Babilon in kawo dukan Babiloniyawa kamar masu gudun hijira, a cikin jiragen ruwa waɗanda suke taƙama da su.
Addu’ar yamma: karatu (domin Waliyyi George)
Ba ya cikin wannan fassara
Addu’ar yamma: karatu (domin Waliyyi George)
Ba ya cikin wannan fassara
Addu’ar asuba: Bishara (domin Waliyyi George)
2Ba abin da yake rufe da ba za a fallasa ba, ko kuma abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba. 3Abin da kuka faɗa a cikin duhu, za a ji shi a hasken rana. Kuma abin da kuka faɗa a kunne, a cikin ɗakunan ciki-ciki, za a yi shelarsa daga kan rufin ɗakuna. 4“Ina dai gaya muku abokaina, kada ku ji tsoron masu kashe jiki, amma bayan haka, ba sauran abin da za su iya yi. 5Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa. 6Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba. 7Tabbatacce, gashin kanku ɗin nan ma, an ƙidaya su duka. Kada ku ji tsoro. Darajarku ta fi na kanari masu yawa girma. 8“Ina gaya muku, duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai shaida shi a gaban mala’ikun Allah. 9Amma wanda ya yi mūsun sanina a gaban mutane, shi ma za a yi mūsunsa a gaban mala’ikun Allah. 10Kuma duk wanda ya faɗi kalmar zagi a kan Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya saɓa wa Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba. 11“Sa’ad da an kai ku a gaban majami’u, da gaban masu mulki, da kuma gaban masu iko, kada ku damu da yadda za ku kāre kanku, ko kuma abin da za ku faɗa, 12gama Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya dace ku faɗa a lokacin.”
Wasiƙa
38Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki. 39Alkawarin dominku ne da ’ya’yanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa, domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.” 40Da waɗansu kalmomi masu yawa ya gargaɗe su; ya kuma roƙe su cewa, “Ku ceci kanku daga wannan lalataccen zamani.” 41Waɗanda suka yarda da saƙonsa kuwa aka yi musu baftisma, a ranar kuwa yawansu ya ƙaru da mutum kusan dubu uku. 42Suka ba da kansu ga koyarwar manzanni da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga addu’a. 43Kowa ya cika da tsoro, manzannin kuwa suka aikata abubuwan banmamaki da alamu masu yawa.
Wasiƙa (domin Waliyyi George)
1Kusan a wannan lokaci ne Sarki Hiridus ya kama waɗansu da suke na ikkilisiya, da niyya ya tsananta musu. 2Ya sa aka kashe Yaƙub, ɗan’uwan Yohanna, da takobi. 3Sa’ad da ya ga wannan ya faranta wa Yahudawa rai, sai ya kama Bitrus shi ma. Wannan ya faru kwanakin Bikin Burodi Marar Yisti. 4Bayan ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, don su yi gadinsa. Hiridus ya yi niyyar ya yi masa shari’a a gaban mutane bayan Bikin Ƙetarewa. 5Saboda haka aka tsare Bitrus a kurkuku, amma ikkilisiya ta nace da addu’a ga Allah dominsa. 6A daren da in gari ya waye da Hiridus yake niyyar kawo shi domin a yi masa shari’a, Bitrus yana barci tsakanin sojoji biyu, daure da sarƙoƙi biyu, masu gadi kuma suna bakin ƙofa. 7Ba zato ba tsammani sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa. 8Sa’an nan mala’ikan ya ce masa, “Ka sa rigunarka da takalmanka.” Bitrus kuwa ya sa. Mala’ikan ya faɗa masa cewa, “Ka yafa mayafinka ka bi ni.” 9Bitrus ya bi shi suka fita kurkukun, amma bai ma san cewa abin da mala’ikan yake yi tabbatacce ne ba; yana tsammani wahayi yake gani. 10Suka wuce masu gadi na fari da na biyu, suka kuma isa ƙofar ƙarfe ta shiga birni. Ƙofar kuwa ta buɗe musu da kanta, suka kuma wuce. Sa’ad da suka yi tafiya tsawon wani titi, nan take mala’ikan ya bar shi. 11Sai Bitrus ya dawo hankalinsa ya ce, “Yanzu na sani ba shakka Ubangiji ne ya aiki mala’ikansa yă cece ni daga hannun Hiridus da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.”
Bishara
1Akwai wani Bafarisiye mai suna Nikodimus, wani ɗan majalisar Yahudawa. 2Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.” 3Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.” 4Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!” 5Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu. 6Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu. 7Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’ 8Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.” 9Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya wannan zai yiwu?” 10Yesu ya ce, “Kai ma da kake malami na Isra’ila, ba ka fahimci waɗannan abubuwa ba? 11Gaskiya nake faɗa maka, muna magana a kan abin da muka sani, muka kuma shaida abin da muka gani ne, amma har yanzu kun ƙi ku karɓi shaidarmu. 12Na yi muku magana a kan abubuwan duniya amma ba ku gaskata ba; to, yaya za ku gaskata in na yi magana a kan abubuwan sama? 13Ba wanda ya taɓa hawa zuwa sama sai wanda ya sauka daga sama, wato, Ɗan Mutum. 14Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum, 15don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.”
Bishara (domin Waliyyi George)
17Umarnina ke nan. Ku ƙaunaci juna. 18“In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne. 19Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. 20Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma. 21Za su yi muku haka saboda sunana, gama ba su san Wannan da ya aiko ni ba. 22Da a ce ban zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Yanzu kam, ba su da wata hujja a kan zunubinsu. 23Wanda ya ƙi ni ya ƙi ya ƙi Ubana ma. 24Da a ce ban yi ayyuka a cikinsu waɗanda babu wani da ya taɓa yi ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun ga waɗannan ayyukan banmamaki, duk da haka sun ƙi ni sun kuma ƙi Ubana. 25Amma wannan ya faru ne domin a cika abin da yake a rubuce cikin Dokarsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’ 26“Sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba, zai ba da shaida game da ni. 27Ku ma dole ku ba da shaida, domin kun kasance tare da ni tun daga farko. 16:1“Na faɗa muku wannan duka, domin kada ku bauɗe. 2Za su kore ku daga majami’a; lalle, lokaci yana zuwa da duk wanda ya kashe ku, zai ɗauka yana yin wa Allah hidima ne.
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Afirilu 23 a kalandar ikilisiya shi ne Mayu 6 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi