Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Afirilu 2027 › Afirilu 17
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Afirilu 17, 2027
Asabar · Mako na 3 na lokacin Ista
Bukukuwa da waliyyai
Asabar a mako na 3 na lokacin Ista
Ranar mako · Launin ibada: fari
Karatun yini
Karatu na farko
31Sa’an nan ikkilisiya ko’ina a Yahudiya, Galili da kuma Samariya ta sami salama. Ta yi ƙarfi; ta kuma ƙarfafa ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ta ƙaru sosai tana rayuwa cikin tsoron Ubangiji. 32Da Bitrus yake zazzaga ƙasar, sai ya je ya ziyarci tsarkakan da suke a Lidda. 33A can ya tarar da wani mutum mai suna Eniyas, shanyayye wanda yake kwance kan gado shekara takwas. 34Sai Bitrus ya ce masa, “Eniyas, Yesu Kiristi ya warkar da kai. Tashi ka naɗe tabarmarka.” Nan da nan Eniyas ya tashi. 35Duk waɗanda suke zama a Lidda da Sharon suka gan shi suka kuma juyo ga Ubangiji. 36A Yoffa akwai wata almajira mai suna Tabita (a harshen Girik sunanta shi ne Dokas); ita mai aikin alheri ce kullum, tana kuma taimakon matalauta. 37A lokacin nan ta yi rashin lafiya ta mutu, aka kuma yi wa gawarta wanka aka ajiye a wani ɗaki a gidan sama. 38Lidda yana kusa da Yoffa; saboda haka sa’ad da almajirai suka ji cewa Bitrus yana a Lidda, sai suka aiki mutum biyu wurinsa su roƙe shi cewa, “In ka yarda ka zo nan da nan!” 39Sai Bitrus ya tafi tare da su, sa’ad da ya iso sai aka kai shi ɗakin saman. Duka gwauraye suka tsaya kewaye da shi, suna kuka suna nunnuna masa riguna da kuma waɗansu tufafin da Dokas ta yi yayinda take tare da su. 40Bitrus ya fitar da su duka daga ɗakin; sa’an nan ya durƙusa ya yi addu’a. Da ya juya wajen matacciyar, sai ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe idanunta, ta ga Bitrus sai ta tashi zaune. 41Ya kama ta a hannu ya taimake ta ta tsaya a ƙafafunta. Sa’an nan ya kira masu bi da kuma gwaurayen ya miƙa musu ita da rai. 42Wannan ya zama sananne ko’ina a Yoffa, mutane da yawa kuma suka gaskata da Ubangiji.
Zaburar amsawa
12Yaya zan sāka wa Ubangiji saboda dukan alherinsa gare ni? 13Zan daga kwaf na ceto in kuma kira ga sunan Ubangiji. 14Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa. 15Abu mai daraja a gaban Ubangiji shi ne mutuwar tsarkakansa. 16Ya Ubangiji, da gaske ni bawanka ne; ni bawanka ne, ɗan baiwarka; ka ’yantar da ni daga sarƙoƙi. 17Zan yi hadayar godiya gare ka in kuma kira bisa sunan Ubangiji.
Bishara
60Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan koyarwa tana da wuya. Wa zai iya yarda da ita?” 61Da yake ya san almajiransa suna gunaguni game da wannan, sai Yesu ya ce musu, “Wannan ya ɓata muku rai ne? 62Me za ku ce ke nan, in kuka gan Ɗan Mutum yana hawa zuwa inda yake dā! 63Ruhu ne yake ba da rai; jikin kam, ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku, Ruhu ne, da kuma rai. 64Duk da haka akwai waɗansunku da ba su gaskata ba.” Gama Yesu ya sani tun farko, waɗanda ba su gaskata ba, da kuma wanda zai bashe shi. 65Ya ci gaba da cewa, “Shi ya sa na faɗa muku cewa ba mai iya zuwa wurina, sai dai Uba ya yardar masa.” 66Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina bin sa. 67Sai Yesu ya tambayi Sha Biyun, “Ku ma za ku tafi ne?” 68Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami. 69Mun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi