Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Maris 2027 › Maris 5

Kalandar Ortodoks · 20 ga Faburairu (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Maris 5, 2027

Juma’a · Makon bankwana da nama · Sauti na 6

Bukukuwa da waliyyai

Juma’a a makon bankwana da nama

Ranar azumi

Ana iya cin kifi

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Wasiƙa

2Yoh 1:1–13

1Dattijon nan, Zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya da kuma ’ya’yanta, waɗanda nake ƙauna ƙwarai da gaske kuma ba ni kaɗai ba, amma har da dukan waɗanda suka san gaskiya. 2Muna ƙaunarku saboda gaskiyan nan, wadda take cikinmu za tă kuma kasance tare da mu har abada. 3Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da kuma Yesu Kiristi, Ɗan Uba, su kasance tare da mu cikin gaskiya da ƙauna. 4Na yi farin ciki ƙwarai, da na sami waɗansu ’ya’yanki suna tafiya cikin gaskiya, kamar yadda Uba ya umarce mu. 5Yanzu kuma, uwargida ƙaunatacciya, ba sabon umarni nake rubuta miki ba sai dai wanda muke da shi tun farko. Ina roƙo cewa mu ƙaunaci juna. 6Ƙauna, ita ce mu yi biyayya ga umarnansa. Kamar yadda kuka ji tun da fari, umarninsa shi ne ku yi zaman ƙauna. 7Masu ruɗi da yawa, waɗanda ba su yarda da zuwan Yesu Kiristi cikin jiki ba, sun riga sun fito a duniya. Duk irin mutumin nan mai ruɗi ne kuma magabcin Kiristi. 8Ku lura don kada ku yi hasarar aikin da kuka yi, sai dai ku sami cikakken lada. 9Duk mutumin da bai tsaya a kan koyarwar Kiristi ba, amma ya yi ƙari a kanta, mutumin nan ba shi da Allah. Amma wanda ya tsaya a kan koyarwar Kiristi, yana da Uban da kuma Ɗan. 10Duk wanda ya zo wurinku bai kuma kawo koyarwan nan ba, kada ku karɓe shi a gidanku ko ku marabce shi. 11Duk wanda ya karɓe shi yana tarayya da mugun aikinsa ke nan. 12Ina da abubuwa da dama da zan rubuta muku, sai dai ba na so in yi amfani da takarda da inki in rubuta. A maimako, ina fata in ziyarce ku in kuma yi magana da ku fuska da fuska, domin farin cikinmu yă zama cikakke. 13’Ya’yan ’yar’uwarki wadda Allah ya keɓe, suna gaishe ku.

Bishara

Mar 15:22, 25, 33–41

22Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai). 25Sa’a ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi. 33Daga sa’a ta shida har zuwa sa’a ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar. 34A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”). 35Da waɗansu cikin waɗanda suke tsattsaye kusa da wurin suka ji haka, suka ce, “Ku saurara, yana kiran Iliya.” 36Wani mutum ya ruga ya je ya jiƙo soso da ruwan tsami, ya soka a sanda ya miƙa wa Yesu yă sha. Ya ce, “Ku ƙyale shi. Bari mu ga ko Iliya zai zo yă saukar da shi.” 37Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe. 38Labulen haikali kuwa ya yage kashi biyu, daga sama har ƙasa. 39Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!” 40Waɗansu mata suna kallo daga nesa. A cikinsu kuwa akwai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub ƙarami da Yusuf, da kuma Salome. 41A Galili waɗannan mata ne suka riƙa bin sa suna yin masa hidima. Waɗansu mata da yawa da suka zo tare da shi daga Urushalima, su ma suna nan a can.

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Faburairu 20 a kalandar ikilisiya shi ne Maris 5 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi