Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Janairu 2027 › Janairu 16

Kalandar Ortodoks · 3 ga Janairu (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Janairu 16, 2027

Asabar · Mako na 33 bayan Fentekos · Sauti na 7

Bukukuwa da waliyyai

Asabar kafin Bayyanuwar Ubangiji

Lokacin Kirsimeti (Svyatki)

Babu azumi

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Wasiƙa (domin Asabar kafin Bayyanuwar Ubangiji)

1Tim 3:14–4:5

14Ko da yake ina sa zuciya zo wurinka nan ba da daɗewa ba, ina rubuta muka waɗannan umarnai domin, 15in na yi jinkiri, za ka san yadda ya kamata mutane su tafiyar da halayensu a cikin jama’ar Allah, wadda take ikkilisiyar Allah rayayye, ginshiƙi da kuma tushen gaskiya. 16Ba shakka, asirin addini da girma yake. Ya bayyana cikin jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, mala’iku suka gan shi, aka yi wa’azinsa cikin al’ummai, aka gaskata shi a duniya, aka ɗauke shi sama cikin ɗaukaka. 4:1Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa. 2Irin koyarwan nan tana zuwa ne daga waɗansu munafukai maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu kaca-kaca. 3Suna hana mutane yin aure suna kuma umarce su kada su ci waɗansu irin abinci, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka gaskata suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya. 4Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau, kada kuma a ƙi kome in dai an karɓe shi da godiya, 5domin an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da kuma addu’a.

Bishara (domin Asabar kafin Bayyanuwar Ubangiji)

Mat 3:1–11

1A waɗancan kwanaki, Yohanna Mai Baftisma ya zo, yana wa’azi a Hamadan Yahudiya 2yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.” 3Wannan shi ne wanda aka yi maganarsa ta wurin annabi Ishaya cewa, “Ga murya mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ” 4Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma daure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da zumar jeji. 5Mutane suka zo wurinsa daga Urushalima da dukan Yahudiya da kuma dukan yankin Urdun. 6Suna furta zunubansu, ya kuma yi musu baftisma a Kogin Urdun. 7Amma da Yohanna ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa inda yake yin baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa? 8Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. 9Kada ma ku yi tunani a ranku cewa, ‘Ai, Ibrahim ne mahaifinmu.’ Ina gaya muku cewa Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim daga cikin duwatsun nan. 10An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta. 11“Ina muku baftisma da ruwa domin tuba. Amma wani yana zuwa a bayana wanda ya fi ni iko, wanda ko takalmansa ma ban isa in ɗauka ba. Zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta.

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Janairu 3 a kalandar ikilisiya shi ne Janairu 16 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi