Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Janairu 2027 › Janairu 1
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Janairu 1, 2027
Juma’a · Lokacin Kirsimeti
Bukukuwa da waliyyai
Maryamu, Uwar Allah Mai Tsarki
Babban biki · Launin ibada: fari
Karatun yini
Karatu na farko
22Ubangiji ya ce wa Musa, 23“Gaya wa Haruna da ’ya’yansa, ‘Ga yadda za ku albarkaci Isra’ilawa. Za ku ce musu, 24“ ‘ “ Ubangiji yă albarkace ku, yă kuma kiyaye ku; 25Ubangiji yă sa fuskarsa ta haskaka a kanku, yă kuma yi muku alheri; 26Ubangiji yă dube ku da idon rahama, yă kuma ba ku salama.” ’ 27“Da haka za su sa sunana a kan Isra’ilawa, ni kuma zan albarkace su.”
Zaburar amsawa
1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura. Waƙa. Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, Sela 2don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai. 4Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. Sela 5Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe. 7Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.
Karatu na biyu
4Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka, 5domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya. 6Da yake ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “ Abba, Uba.” 7Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.
Bishara
16Sai suka tafi da sauri, suka tarar da Maryamu da Yusuf, da kuma jaririn kwance a kwami. 17Sa’ad da suka gan shi, sai suka baza maganar da aka gaya musu game da yaron, 18duk kuwa waɗanda suka ji wannan, suka yi mamaki a kan abin da makiyayan suka faɗa. 19Amma Maryamu ta riƙe dukan waɗannan abubuwa ta kuma yi ta tunaninsu a zuciyarta. 20Makiyayan kuwa suka koma, suna ɗaukaka suna kuma yabon Allah saboda dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu. 21A rana ta takwas, da lokaci ya yi da za a yi masa kaciya, sai aka ba shi suna Yesu, sunan da mala’ika ya ba shi kafin a yi cikinsa.
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi