Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2026 › Disamba 21

Kalandar Ortodoks · 8 ga Disamba (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Disamba 21, 2026

Litinin · Mako na 30 bayan Fentekos · Sauti na 4

Bukukuwa da waliyyai

Venerable Patapios of Thebes (7th C)

Azumin Haihuwar Kiristi

Azumi: dafaffen abinci ba tare da mai ba

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Wasiƙa

Ibr 8:7–13

7Gama da a ce alkawari na fari ba shi da wani laifi, da ba sai an sāke neman wani ba. 8Amma Allah ya sami mutane da laifi ya ce, “Ina gaya muku lokaci yana zuwa, sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda. 9Ba zai zama kamar irin alkawarin da na yi da kakanni-kakanninsu sa’ad da na kama hannunsu don in fitar da su daga Masar ba, domin ba su yi aminci da alkawarina ba, sai na juya musu baya, in ji Ubangiji. 10Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila, bayan lokacin nan, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu. Zan zama Allahnsu, su kuwa za su zama mutanena. 11Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba, balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin dukansu za su san ni, daga ƙaraminsu zuwa babba. 12Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba.” 13Ta wurin kira wannan alkawari “sabo,” ya mai da na farin tsoho ke nan; abin da yake tsoho yana kuma daɗa tsufa, zai shuɗe nan ba da daɗewa ba.

Bishara

Luk 20:27–44

27Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa, 28“Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba ’ya’ya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.’ 29To, an yi waɗansu ’yan’uwa bakwai. Na fari ya auri wata mace, ya mutu ba ’ya’ya. 30Na biyun, 31da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu ’ya’ya. 32A ƙarshe, ita macen ma ta mutu. 33Shin, a tashin matattu, matar wa za tă zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.” 34Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure, 35amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba. 36Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su ’ya’yan Allah ne, tun da su ’ya’yan tashin matattu ne. 37Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’ 38Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.” 39Sai waɗansu malaman dokoki suka amsa suka ce, “Ka faɗi daidai, malam!” 40Kuma ba wanda ya sami ƙarfin halin yin masa waɗansu tambayoyi. 41Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’ 42Dawuda da kansa ya faɗa a cikin Zabura, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, 43sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’ 44Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji.’ Ta, yaya zai zama ɗansa?”

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Disamba 8 a kalandar ikilisiya shi ne Disamba 21 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi