Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2026 › Disamba 13
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Disamba 13, 2026
Lahadi · Mako na 3 na lokacin Zuwan Ubangiji
Bukukuwa da waliyyai
Lahadi ta 3 ta lokacin Zuwan Ubangiji
Lahadi · Launin ibada: ruwan hoda
Karatun yini
Karatu na farko
1Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu 2don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu, don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki, 10Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji; raina yana farin ciki a cikin Allahna. Gama ya suturce ni da rigunan ceto ya yi mini ado da rigar adalci, yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja. 11Gama kamar yadda ƙasa takan sa tsire-tsire su tohu lambu kuma ya sa iri ya yi girma, haka Ubangiji Mai Iko Duka zai sa adalci da yabo su tsiro a gaban dukan al’ummai.
Zaburar amsawa
47ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona, 48gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa. Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka, 49gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa, sunansa labudda Mai Tsarki ne. 50Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa, daga zamani zuwa zamani. 53Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa amma ya sallami mawadata hannu wofi. 54Ya taimaki bawansa Isra’ila, yana tunawa yă nuna jinƙai
Karatu na biyu
16Ku riƙa farin ciki kullum; 17ku ci gaba da yin addu’a; 18ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu. 19Kada ku danne aikin Ruhu. 20Kada ku rena annabci, 21amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau, 22ku ƙi kowace mugunta. 23Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 24Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.
Bishara
6Akwai wani mutumin da aka aiko daga Allah; mai suna Yohanna. 7Ya zo a matsayin mai shaida domin yă ba da shaida game da wannan haske, don ta wurinsa dukan mutane su ba da gaskiya. 8Shi kansa ba shi ne hasken ba; sai dai ya zo a matsayin shaida ne kaɗai ga hasken. 19To, ga shaidar Yohanna sa’ad da Yahudawan Urushalima suka aiki firistoci da Lawiyawa su tambaye shi ko shi wane ne. 20Bai yi mūsu ba, amma ya shaida a fili cewa, “Ba ni ne Kiristi ba.” 21Sai suka tambaye shi suka ce, “To, wane ne kai? Kai ne Iliya?” Ya ce, “A’a, ni ba shi ba ne.” “Kai ne Annabin nan?” Ya amsa ya ce, “A’a.” 22A ƙarshe suka ce, “Wane ne kai? Ka ba mu amsa don mu mayar wa waɗanda suka aike mu. Me kake ce da kanka?” 23Yohanna ya amsa da kalmomin annabi Ishaya, “Ni murya ne mai kira a hamada, ‘Ku miƙe hanya domin Ubangiji.’ ” 24To, waɗansu Farisiyawan da aka aika 25suka tambaye shi suka ce, “Don me kake yin baftisma in kai ba Kiristi ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?” 26Yohanna ya amsa ya ce, “Ni dai ina baftisma da ruwa ne, amma a cikinku akwai wani tsaye da ba ku sani ba. 27Shi ne mai zuwa bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.” 28Wannan duk ya faru ne a Betani a ƙetaren Urdun, inda Yohanna yake yin baftisma.
Tsarkakan ranar
- Waliyya Lucy, budurwa kuma shahidiya
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi