Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2026 › Disamba 5

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Disamba 5, 2026

Asabar · Mako na 1 na lokacin Zuwan Ubangiji

Bukukuwa da waliyyai

Asabar a mako na 1 na lokacin Zuwan Ubangiji

Ranar mako · Launin ibada: shunayya

Karatun yini

Karatu na farko

Ish 30:19–21, 23–26

19Ya mutanen Sihiyona, waɗanda suke zama a Urushalima, ba za ku ƙara kuka ba. Zai zama mai alheri sa’ad da kuka yi kukan neman taimako! Da zarar ya ji, zai amsa muku. 20Ko da yake Ubangiji yakan ba da abincin azaba da ruwan wahala, ba za a ƙara ɓoye malamanku ba; da idanunku za ku gan su. 21Ko kun juye dama ko hagu, kunnuwanku za su ji murya a bayanku tana cewa, “Ga hanya; ku yi tafiya a kai.” 23Zai kuma aiko muku da ruwan sama don shuki a ƙasa, kuma abincin da zai fito daga gona zai zama mai albarka da kuma mai yawa. A wannan rana shanu za su yi kiwo a wadatacciyar makiyaya. 24Shanunku da jakunanku da suke huɗar gonakinku za su ci harawa mafi kyau, wanda an sheƙe shi da babban cokali mai yatsu da kuma babban cokali. 25A ranar babban kisa, sa’ad da hasumiyoyi za su fāɗi, rafuffukan ruwa za su malalo a kan kowane dutse da kowane tudu mai tsawo. 26Wata zai yi haske kamar rana, kuma hasken rana zai ma yi sau bakwai na haskenta, kamar hasken cikakku ranaku bakwai, sa’ad da Ubangiji zai ɗaura raunukan mutanensa ya kuma warkar da raunukan da ya yi musu.

Zaburar amsawa

Zab 147:1–6

1Yabi Ubangiji. Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu, abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi! 2Ubangiji ya gina Urushalima; ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta. 3Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu. 4Ya lissafta yawan taurari ya kuma kira kowannensu da suna. 5Shugabanmu mai girma ne mai iko duka; ganewarsa ba shi da iyaka. 6Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai yakan yar da mugaye a ƙasa.

Bishara

Mat 9:35–10:1, 6–8

35Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. 36Da ya ga taron mutane, sai ya ji tausayinsu, domin an wulaƙanta su ba su kuma da mai taimako, kamar tumaki marasa makiyayi. 37Sai ya ce wa almajiransa, “Girbi yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. 38Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi, yă aiko da ma’aikata cikin gonarsa na girbi.” 10:1Sai ya kira almajiransa goma sha biyu wurinsa ya kuma ba su iko su fitar aljanu, su kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. 6A maimakon haka ku je wajen ɓatattun tumakin Isra’ila. 7Sa’ad da kuke tafiya, ku yi wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin sama ya kusato.’ 8Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi