Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2026 › Nuwamba 25
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Nuwamba 25, 2026
Laraba · Mako na 34 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Laraba a mako na 34 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Waliyya Catherine ta Alekzandariya, budurwa kuma shahidiya · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
1Na ga wata babbar alama mai banmamaki a sama, mala’iku bakwai da annobai bakwai na ƙarshe, na ƙarshe, domin da su ne fushin Allah ya cika. 2Sai na ga abin da ya yi kamar tekun gilashi gauraye da wuta kuma tsaye kusa da teku, waɗanda suka ci nasara bisan dabbar da siffarta da bisan lambar sunanta. Suna riƙe da garayu waɗanda Allah ya ba su 3suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa, “Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki, ya Ubangiji Maɗaukaki. Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya, ya Sarkin zamanai. 4Wane ne ba zai ji tsoronka, yă kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji? Gama kai kaɗai ne mai tsarki. Dukan al’ummai za su zo su yi sujada a gabanka, gama an bayyana ayyukan adalcinka.”
Zaburar amsawa
1Zabura ce. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto. 2Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai. 3Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu. 7Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa, duniya da kuma kome da yake cikinta. 8Bari koguna su tafa hannuwansu, bari duwatsu su rera tare don farin ciki; 9bari su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa domin yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya da adalci mutane kuma cikin gaskiya.
Bishara
12“Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majami’u, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana. 13Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su. 14Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku. 15Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata. 16Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku. 17Duk mutane za su ƙi ku saboda ni. 18Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba. 19Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.
Tsarkakan ranar
- Waliyya Catherine ta Alekzandariya, budurwa kuma shahidiya
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi