Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2026 › Oktoba 29
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 29, 2026
Alhamis · Mako na 30 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Alhamis a mako na 30 na lokacin yau da kullum
Ranar mako · Launin ibada: kore
Karatun yini
Karatu na farko
10A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi. 11Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. 12Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. 13Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge. 14Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, 15shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku. 16Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. 17Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah. 18A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a. 19Ku kuma yi addu’a domina, don duk sa’ad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro, don in sanar da asirin bishara, 20wadda nake jakadanta cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a don in iya yin shelarta babu tsoro, yadda ya kamata in yi.
Zaburar amsawa
1Ta Dawuda. Yabo ya tabbata ga Ubangiji dutsena, wanda ya horar da hannuwana don yaƙi, yatsotsina don faɗa. 2Shi ne Allah mai ƙaunata da kuma kagarata, katangata da mai cetona, garkuwata, wanda nake neman mafaka daga gare shi, wanda ya sa mutane a ƙarƙashina. 9Zan rera sabuwar waƙa gare ka, ya Allah; a kan molo mai tsirkiya goma zan yi maka kiɗi, 10ga Wannan wanda yake ba wa sarakuna nasara, wanda ya cece bawansa Dawuda. Daga takobin kisa.
Bishara
31A wannan lokaci, waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce wa Yesu, “Ka bar nan ka tafi wani wuri dabam. Hiridus yana so ya kashe ka.” 32Ya amsa ya ce, “Ku je ku gaya wa dilan nan, wato, mai makirci cewa, ‘Da yau da kuma gobe, zan fitar da aljanu, in kuma warkar da mutane, sa’an nan a rana ta uku in cika burin aikina. 33Duk da haka, dole in ci gaba da aikin a yau, da kuma gobe, sa’an nan in ci gaba da yin haka kashegari kuma, gama tabbatacce, ba annabi da yakan mutu a bayan birnin Urushalima!’ 34“Urushalima, ayya Urushalima, ke da kika kashe annabawa, kuma kika jefa wa waɗanda aka aika gare ki da duwatsu. Sau da yawa na yi kewan in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, kamar yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma ba ki yarda ba! 35Duba, an bar muku gidanku fanko. Ina kuwa faɗa muku, ba za ku sāke ganina ba, sai kun ce, ‘Mai albarka ne shi wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ”
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi