Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2026 › Oktoba 28
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 28, 2026
Laraba · Mako na 30 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Waliyyi Siman da Waliyyi Yahuda, manzanni
Biki · Launin ibada: ja
Karatun yini
Karatu na farko
19Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ’yan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma. 20Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci na ginin. 21Ta wurinsa ne dukan ginin yake a haɗe, shi ne kuma yake sa ginin yă yi girma, yă zama haikali mai tsarki domin Ubangiji. 22Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa.
Zaburar amsawa
1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sammai suna shelar ɗaukakar Allah; sararin sama suna furta aikin hannuwansa. 2Kowace rana tana yin jawabi; kowane dare yana nuna sani. 3Ba magana, ba kalmar da aka hurta, ba wani amon da aka ji daga gare su. 4Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya, kalmominsu zuwa iyakokin duniya. A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,
Bishara
12Wata rana, a cikin kwanakin nan, Yesu ya je wani dutse domin yă yi addu’a, ya kuma kwana yana addu’a ga Allah. 13Da gari ya waye, sai ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya zaɓi guda goma sha biyu daga cikinsu, waɗanda ya kira su, Manzanni. 14Siman (wanda ya kira Bitrus), ɗan’uwansa Andarawus, Yaƙub, Yohanna, Filibus, Bartolomeyu, 15Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Siman wanda ake kira Zilot, 16Yahuda ɗan Yaƙub, da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu. 17Sai ya sauko tare da su, ya tsaya a wani fili. A can, akwai taro mai yawa na almajiransa, da kuma mutane masu yawan gaske daga ko’ina a Yahudiya, Urushalima da kuma Taya da Sidon da suke bakin teku, 18waɗanda suka zo domin su ji shi, a kuma warkar da cututtukansu. Waɗanda suke fama da mugayen ruhohi kuwa aka warkar da su. 19Kuma dukan mutane suka yi ƙoƙari su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Siman da Waliyyi Yahuda, manzanni
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi