Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2026 › Oktoba 22
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 22, 2026
Alhamis · Mako na 29 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Alhamis a mako na 29 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Waliyyi John Paul na II, Fafaroma · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
14Saboda wannan ne nake a durƙushe a gaban Uba, 15wanda ya ba wa kowane iyali a sama da ƙasa suna. 16Ina addu’a cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa. 17Ina addu’a domin Kiristi yă zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu’a saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna, 18don ku sami iko, tare da dukan tsarkaka, ku fahimci fāɗi, tsawo, da kuma zurfin ƙaunar Kiristi take. 19Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan cikar Allah. 20Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi shi wanda yake da ikon yin aiki a cikinmu, yana kuma aikata abubuwa fiye da dukan abin da muke roƙo, ko muke tunani. 21Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikkilisiya da kuma a cikin Kiristi Yesu, har yă zuwa dukan zamanai, har abada abadin! Amin.
Zaburar amsawa
1Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai; daidai ne masu gaskiya su yabe shi. 2Ku yabi Ubangiji da garaya; ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma. 4Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya; yana da aminci cikin kome da yake yi. 5Ubangiji yana ƙaunar adalci duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa. 11Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada, manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai. 12Mai farin ciki ce al’ummar da Allah ne Ubangijinta, mutanen da ya zaɓa don gādonsa. 18Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa, a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa, 19don yă cece su daga mutuwa ya bar su da rai a lokacin yunwa.
Bishara
49“Na zo ne domin in kawo wuta a duniya. Ina so da ta riga ta ƙunu! 50Amma ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa damu sosai, sai na kammala ta! 51Kuna tsammani na zo domin in kawo salama a duniya ne? A’a! Ina gaya muku, rabuwa ne. 52Daga yanzu, za a iske mutum biyar a gida ɗaya sun rabu, suna gāba da juna, uku suna gāba da biyu, biyun suna gāba da ukun. 53Za su rarrabu. Mahaifi yana gāba da ɗan, ɗan kuma yana gāba da mahaifin. Mahaifiya tana gāba da diyar, diyar kuma tana gāba da mahaifiyar. Suruka tana gāba da matar ɗa, matar ɗa kuma tana gāba da suruka.”
Tsarkakan ranar
- Waliyyi John Paul na II, Fafaroma
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi A, shekarar ranakun mako II.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi