Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2026 › Oktoba 10
Kalandar Ortodoks · 27 ga Satumba (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Oktoba 10, 2026
Asabar · Mako na 19 bayan Fentekos · Sauti na 1
Bukukuwa da waliyyai
Martyr Callistratus and 49 Martyrs in his company († 304)
Azumi
Babu azumi
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Wasiƙa (domin Juma’a)
27Kome ya faru, ku yi zaman da ya cancanci bisharar Kiristi. Ta haka, ko na zo na gan ku, ko ban zo ba, in ji labari cewa kun tsaya da ƙarfi a cikin ruhu ɗaya, kuna fama kamar mutum ɗaya saboda bangaskiyar bishara 28ba tare da kun ji tsoron waɗanda suke gāba da ku ta kowace hanya ba. Wannan alama ce a gare su cewa za a hallaka su, amma a gare ku za a cece ku, wannan tabbacin kuwa daga wurin Allah ne. 29Gama an ba ku zarafi a madadin Kiristi cewa ba gaskatawa da shi kaɗai ba kuka yi ba, har ma ku sha wahala dominsa, 30da yake kuna shan faman da kuka gan na sha, kuna kuma jin cewa har yanzu ina sha. 2:1In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi, 2to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa. 3Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku. 4Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma.
Wasiƙa
58Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba. 16:1To, game da tara kuɗi domin taimakon mutanen Allah, ku yi abin da na gaya wa ikkilisiyoyin Galatiyawa. 2A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba. 3In kuwa na iso sai in ba da wasiƙun gabatarwa ga mutanen da kuka amince da su, in kuma aike su da taimakonku zuwa Urushalima.
Bishara (domin Juma’a)
22Duk suka yabe shi, suka yi mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suka yi tambaya, suna cewa, “Anya, wannan ba ɗan Yusuf ba ne?” 23Yesu ya ce musu, “Tabbatacce, na san za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka! Ka kuma yi abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, a nan garinka.’ ” 24Ya ci gaba, da ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, babu annabin da ake yarda da shi a garinsa. 25Ina tabbatar muku a zamanin Iliya, akwai gwauraye da yawa a Isra’ila, sa’ad da aka rufe sararin sama har shekara uku da rabi, aka kuma yi yunwa mai tsanani ko’ina a ƙasar. 26Duk da haka, ba a aiki Iliya ga ko ɗaya a cikinsu ba. Sai dai zuwa ga wata gwauruwa da take a Zarefat, a yankin Sidon. 27Akwai kuma mutane da yawa a Isra’ila masu kuturta a zamanin annabi Elisha, amma ba ko ɗayansu da aka tsarkake sai Na’aman mutumin Suriyan nan kaɗai.” 28Dukan mutanen da suke cikin majami’a suka fusata ƙwarai da jin wannan. 29Suka tashi, suka fitar da Yesu bayan gari, suka kai shi goshin tudun da aka gina garin, don su ture shi ƙasa, 30amma sai ya bi ta tsakiyar taron ya yi tafiyarsa.
Bishara
31Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a Galili, a ranar Asabbaci kuma, ya fara koya wa mutane. 32Suka yi ta mamakin koyarwarsa, domin saƙonsa yana da iko. 33A cikin majami’ar, akwai wani mutum mai aljani, wani mugun ruhu. Mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, 34“Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki na Allah!” 35Yesu ya tsawata masa da ƙarfin cewa, “Yi shiru! Ka fita daga cikinsa!” Sai aljanin ya fyaɗa mutumin da ƙasa a gabansu duka, sa’an nan ya fita, ya bar shi ba wani rauni. 36Dukan mutanen suka yi mamaki, suka ce wa junansu, “Wace irin koyarwa ce haka? Da ƙarfi da iko, yana ba wa mugayen ruhohin umarni suna kuma fita!”
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Satumba 27 a kalandar ikilisiya shi ne Oktoba 10 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi