Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Daga Hezekiya zuwa Yosiya

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Daga Hezekiya zuwa Yosiya

Mutuwar Yosiya

2Sar 23:28–30 · 2Tar 35:20–27

2 Sarakuna

2Sar 23:28–30

28Game da sauran ayyukan mulkin Yosiya, da duk abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.

29Yayinda Yosiya yake sarki, Fir’auna Neko, sarkin Masar ya haura zuwa Kogin Yuferites don yă taimaki sarkin Assuriya da yaƙi. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa’ad da Fir’auna Neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Megiddo.

30Bayin Yosiya suka ɗauko gawarsa daga Megiddo suka kai Urushalima, suka binne shi a kabarinsa. Sai mutanen ƙasar suka ɗauki Yehoyahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki a madadin mahaifinsa.

2 Tarihi

2Tar 35:20–27

20Bayan wannan duka, sa’ad da Yosiya ya shirya haikali, Neko sarkin Masar ya haura don yă yi yaƙi a Karkemish a Yuferites, sai Yosiya ya fita don yă fafata da shi a yaƙi.

21Amma Neko ya aiki ’yan saƙo ga Yosiya, yana cewa, “Me ya gama ni da kai, ya Sarkin Yahuda? Ban zo in yi yaƙi da kai ba. Na zo ne in yi yaƙi da gidan da yake gāba da ni! Ka ƙyale ni! Allah ne ya riga ya faɗa mini in hanzarta. Kada ka yi gāba da Allah, wanda yake tare da ni, don kada yă hallaka ka.”

22Yosiya fa, bai juya daga gare shi ba, amma ya ɓad da kama don yă yi yaƙin. Bai saurari abin da Neko ya faɗa bisa ga umarnin Allah ba, amma ya tafi ya yaƙe shi a filin Megiddo.

23Maharba suka harbi Yosiya, sai ya ce wa hafsoshinsa, “Ku ɗauke ni ku fita da ni daga nan; gama an yi mini mummunan rauni.”

24Saboda haka suka ɗauke shi a keken yaƙin, suka fitar da shi, suka sa shi a wata keken yaƙin da yake da shi, suka kawo shi Urushalima, inda ya mutu. Aka binne shi a makabartar kakanninsa, sai dukan Yahuda da Urushalima suka yi makoki dominsa.

25Annabin Irmiya ya tsara waƙoƙin makoki domin Yosiya, wanda har wa yau mawaƙa maza da mata suke rera game da Yosiya. Suka sa waɗannan su zama al’ada a Isra’ila, suna kuma a rubuce cikin Littafin Makoki.

26Sauran ayyukan mulkin Yosiya da kuma kyawawan abubuwan da ya yi, bisa ga abin da aka rubuta a Dokar Ubangiji,

27dukan ayyukan, daga farko har zuwa ƙarshe, suna a rubuce cikin littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY