Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Solomon

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Solomon

Solomon ya roƙi hikima a Gibeyon

1Sar 3:4–15 · 2Tar 1:2–13

1 Sarakuna

1Sar 3:4–15

4Sai sarki Solomon ya tafi Gibeyon don yă miƙa hadayu, gama a can ne wuri mafi muhimmanci na sujada. Solomon kuwa ya miƙa hadayun ƙonawa guda dubu a kan wannan bagade.

5A Gibeyon, Ubangiji ya bayyana ga Solomon da dare a mafarki, Allah ya ce, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”

6Solomon ya amsa ya ce, “Ka nuna alheri mai girma ga bawanka, mahaifina Dawuda domin ya yi aminci gare ka da adalci, ya kuma kasance da zuciya mai gaskiya. Ka ci gaba da wannan alheri mai girma gare shi, ka ba shi ɗa don yă zauna a kujerar sarautarsa a wannan rana.

7“Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka sa bawanka a wurin mahaifina Dawuda. Amma ni ɗan yaro ne kawai, ban kuma san yadda zan yi ayyukana ba.

8Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta.

9Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?”

10Sai Ubangiji ya ji daɗi cewa Solomon ya roƙa wannan.

11Saboda haka Allah ya ce masa, “Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya,

12zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba.

13Ban da haka ma, zan ba ka abin da ba ka nema ba; arziki da girma, don a rayuwarka ba za ka kasance da wani kamar ka ba a cikin sarakuna.

14In kuma ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi biyayya da farillaina da umarnaina kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, zan ba ka tsawon rai.”

15Sai Solomon ya farka, ya gane ashe mafarki ne. Ya koma Urushalima, ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji ya miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama. Sa’an nan ya shirya wa fadawansa biki.

2 Tarihi

2Tar 1:2–13

2Sai Solomon ya yi magana ga dukan Isra’ila, ga shugabannin mayaƙa dubu-dubu da shugabannin mayaƙa ɗari-ɗari, ga alƙalai da kuma ga dukan shugabanni a Isra’ila, kawunan iyalai,

3Solomon tare da dukan taron suka tafi masujadan kan tudu a Gibeyon, gama Tentin Sujadar Allah yana can, wanda Musa bawan Ubangiji ya yi a hamada.

4Dawuda ya riga ya haura da akwatin alkawarin Allah daga Kiriyat Yeyarim zuwa inda ya shirya dominsa, domin yă kafa masa tenti a Urushalima.

5Amma bagaden tagullar da Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, ya yi a Gibeyon a gaba tabanakul na Ubangiji; saboda haka Solomon da taron suka neme nufin Ubangiji a can.

6Solomon ya haura zuwa bagaden tagulla a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada, ya kuma miƙa hadayu na ƙonawa dubbai a kansa.

7A wannan dare Allah ya bayyana ga Solomon, ya ce masa, “Roƙi duk abin da kake so in ba ka.”

8Solomon ya amsa wa Allah, “Ka nuna alheri mai girma ga Dawuda mahaifina ka kuma naɗa ni sarki a matsayinsa.

9To, yanzu, ya Ubangiji Allah, ka cika alkawarin da ka yi ga mahaifina Dawuda yă tabbata, gama ka naɗa ni sarki a bisa mutanen da suka wuce ƙirge kamar ƙurar ƙasa.

10Ka ba ni hikima da sani, don in iya jagorance wannan mutane, gama wa zai iya shugabance wannan jama’arka mai girma?”

11Allah ya ce wa Solomon, “Da yake wannan ne sha’awar zuciyarka, ba ka kuwa nemi wadata, arziki ko girma ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, da yake kuma ba ka nemi tsawon rai ba, amma ka nemi hikima da sani don ka shugabanci jama’ata wadda na naɗa ka sarki,

12saboda haka za a ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka wadata, arziki da girma, waɗanda babu wani sarki kafin kai da ya taɓa kasance da su kuma babu wani a bayanka da zai kasance da su.”

13Sa’an nan Solomon ya tafi Urushalima daga masujadar kan tudu a Gibeyon, da kuma daga gaban Tentin Sujada. Ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY