Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Solomon

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Solomon

Addu’ar Solomon a bikin keɓe haikali

1Sar 8:22–53 · 2Tar 6:12–42

1 Sarakuna

1Sar 8:22–53

22Sai Solomon ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji, a gaban dukan taron Isra’ila, ya ɗaga hannuwansa sama,

23ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama can bisa, ko a ƙasa can ƙarƙashi, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna ga bayinka waɗanda suke cin gaba a hanyarka da dukan zuciyarsu.

24Ka kiyaye alkawarinka da ka yi wa bawanka Dawuda mahaifina. Da bakinka ka yi alkawari, da hannunka kuma ka cika shi, yadda yake a yau.

25“Yanzu, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari ka cika wa bawanka Dawuda mahaifina alkawaran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza sun yi hankali cikin dukan abubuwan da suke yi, don su yi tafiya a gabana kamar yadda ka yi.’

26Yanzu fa, ya Allah na Isra’ila, bari maganarka da ka yi wa bawanka Dawuda mahaifina tă cika.

27“Amma anya, Allah, za ka zauna a duniya? Sammai, har ma da saman sammai ba za tă iya riƙe ka ba, balle wannan haikalin da na gina!

28Duk da haka ka ji addu’ar bawanka da kuma roƙonsa don jinƙai, ya Ubangiji Allahna. Ka ji kuka da addu’ar da bawanka yake yi a gabanka a wannan rana.

29Bari idanunka su buɗe, su fuskanci wannan haikali dare da rana, wannan wurin da ka ce, ‘Sunana zai kasance a can,’ saboda ka ji addu’ar bawanka in yana fuskantar wannan wuri.

30Ka ji roƙon bawanka da kuma na mutanenka Isra’ila sa’ad da suka yi addu’a, suka fuskanci wannan wuri. Ka ji daga sama, mazauninka, kuma sa’ad da ka ji, ka gafarta.

31“Sa’ad da mutum ya yi abin da ba daidai ba ga maƙwabcinsa, an kuma bukace shi yă yi rantsuwa, sai ya zo ya rantse a gaban bagade a cikin haikalin nan,

32sai ka ji daga sama, ka kuma yi wani abu. Ka shari’anta tsakanin bayinka, ka hukunta mai laifi, ka mai da laifinsa a kansa, mai gaskiya kuma ka nuna shi marar laifi ne bisa ga gaskiyarsa.

33“Sa’ad da abokan gāba suka ci mutanenka Isra’ila a yaƙi saboda sun yi maka zunubi, sa’ad da kuma suka dawo gare ka don su furta sunanka, suna addu’a suna roƙo gare ka a wannan haikali,

34ka ji daga sama, ka gafarta zunubin mutanenka, ka kuma dawo da su ƙasar da ka ba wa kakanninsu.

35“Sa’ad da sammai sun kulle, babu kuma ruwan sama domin mutane sun yi maka zunubi, sa’ad da suka yi addu’a suna fuskantar wannan wuri, suka kuma furta sunanka, suka juye daga zunubinsu domin ka hore su,

36ka ji daga sama, ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace ta rayuwa, ka kuma aika da ruwan sama a ƙasar da ka ba wa mutanenka gādo.

37“Sa’ad da yunwa ko annoba ta fāɗo a ƙasar, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fāri, ko tsutsa, ko kuwa abokan gāba sun yi musu kwanto, a wani daga cikin biranensu, duk wata cuta, ko ciwon da ya zo,

38in suka yi addu’a ko roƙo ta wurin wani daga cikin mutanenka Isra’ila, kowa ya san wahalar zuciyarsa, ya kuma buɗe hannuwansa yana fuskantar wannan haikali,

39sai ka ji daga sama, mazauninka. Ka gafarta, ka kuma yi wani abu. Ka yi da kowane mutum bisa ga dukan abin da ya yi, tun da yake ka san zuciyarsa (gama kai kaɗai ka san zukatan dukan mutane),

40saboda su ji tsoronka a kowane lokacin da suke zaune a ƙasar da ka ba wa kakanninmu.

41“Game da baƙo kuwa wanda shi ba na mutanenka Isra’ila ba, amma ya zo daga ƙasa mai nisa saboda sunanka,

42gama mutane za su ji game da girman sunanka, da ƙarfin hannunka, da kuma hannunka mai iko, sa’ad da ya zo, ya yi addu’a yana fuskantar wannan haikali,

43ka ji daga sama, mazauninka, ka kuma yi dukan abin da baƙon ya tambaye ka, saboda dukan mutanen duniya su san sunanka, su kuma ji tsoronka, kamar yadda mutanenka Isra’ila suke yi, bari kuma su san cewa wannan gidan da na gina, ya amsa Sunanka.

44“Sa’ad da mutanenka suka tafi yaƙi da abokan gābansu, a duk inda ka aike su, sa’ad da kuma suka yi addu’a ga Ubangiji suna fuskantar birnin da ka zaɓa, da kuma haikalin da na gina domin Sunanka,

45ka ji addu’arsu da roƙonsu daga sama, ka kuma biya musu bukatansu.

46“Sa’ad da suka yi maka zunubi, gama babu wanda ba ya zunubi, ka kuwa yi fushi da su, ka kuma ba da su ga abokin gāba, wanda ya kwashe su kamammu zuwa ƙasarsa, nesa ko kusa;

47in suka canja zuciyarsu a ƙasar da aka riƙe su kamammu, suka tuba, suka kuma roƙe ka a ƙasar waɗanda suka ci su da yaƙi, suka ce, ‘Mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba, mun yi mugunta’;

48in sun juye gare ka da dukan zuciyarsu, da dukan ransu a ƙasar abokan gābansu waɗanda suka kwashe kamammu, suka yi addu’a gare ka, suka fuskanci wajen ƙasar da ka ba wa kakanninsu, waje birnin da ka zaɓa, da kuma haikalin da na gina domin Sunanka;

49sai ka ji daga sama, mazauninka, ka ji addu’a da roƙonsu, ka kuma biya musu bukatansu.

50Ka gafarta wa mutanenka, waɗanda suka yi maka zunubi; ka gafarta dukan laifofin da suka yi maka, ka kuma sa waɗanda suka ci su a yaƙi su ji tausayinsu.

51Gama su mutanenka ne, abin gādonka, waɗanda ka fitar daga Masar, daga tanderu mai narken ƙarfe.

52“Bari idanunka su buɗe ga roƙon bawanka, ga roƙon mutanenka Isra’ila, bari kuma ka saurare su sa’ad da suka yi kuka gare ka.

53Gama ka ware su daga dukan al’umman duniya su zama abin gādonka, kamar yadda aka furta ta wurin bawanka Musa sa’ad da kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka ka fitar da kakanninmu daga Masar.”

2 Tarihi

2Tar 6:12–42

12Sa’an nan Solomon ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron Isra’ila ya ɗaga hannuwansa sama.

13Dā ma ya riga ya gina dakalin tagulla, mai tsawo kamu biyar, fāɗi kamu biyar da kuma tsayi kamu uku, ya kuma sa shi a tsakiyar filin waje. Ya tsaya a kan dakalin ya kuma durƙusa a gaban dukan taron Isra’ila ya buɗe hannuwansa sama.

14Ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama da kuma ƙasa, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna tare da bayinka waɗanda suke cin gaba da zuciya ɗaya a hanyarka.

15Ka kiyaye alkawarinka ga bawanka Dawuda mahaifina; da bakinka ka yi alkawari kuma da hannunka ka cika shi, yadda yake a yau.

16“Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka kiyaye wa bawanka Dawuda mahaifina alkawuran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka kāsa kasance da mutumin da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza za su kula cikin dukan abin da suke yi su yi tafiya a gabana bisa ga dokata, kamar yadda ka yi.’

17Yanzu kuwa, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari maganarka da ka yi alkawarta wa bawanka Dawuda yă cika.

18“Amma tabbatacce Allah zai zauna a duniya tare da mutane? Sammai, har ma da saman sammai, ba za su iya riƙe ka ba. Balle wannan haikalin da na gina!

19Duk da haka ka mai da hankali ga addu’ar bawanka da kuma roƙo don jinƙai, ya Ubangiji, Allahna. Ka ji kuka da addu’ar da bawanka yake yi a gabanka.

20Bari idanunka su buɗu ta wajen wannan haikali dare da rana, wannan wurin da ka ce za ka sa Sunanka a can. Bari ka ji addu’ar da bawanka ke yi ta wajen wannan wuri.

21Ka ji roƙe-roƙen bawanka da na mutanenka Isra’ila sa’ad da suka yi addu’a suna duban wajen wannan wuri. Ka ji daga sama, mazauninka; kuma sa’ad da ka ji, ka gafarta.

22“Sa’ad da mutum ya yi wa maƙwabcinsa laifi aka kuma bukaci ya yi rantsuwa, ya kuma zo ya rantse a gaban bagadenka a cikin wannan haikali,

23sai ka ji daga sama ka kuma yi wani abu. Ka shari’anta tsakanin bayinka, kana sāka wa mai laifi ta wurin kawo a kansa hakkin abin da ya yi. Ka nuna cewa marar laifi ba shi da laifi, ta haka a fiffita rashin laifinsa.

24“Sa’ad da an ci mutanenka Isra’ila a yaƙi ta wurin abokin gāba domin sun yi maka zunubi kuma sa’ad da suka juya suka furta sunanka, suna addu’a suka kuma yin roƙe-roƙe a gabanka a wannan haikali,

25sai ka ji daga sama ka kuma gafarta zunubin mutanenka Isra’ila ka kuma dawo da su zuwa ƙasar da ka ba su da kuma kakanninsu.

26“Sa’ad da sammai suka rufu ba kuwa ruwan sama saboda mutanenka sun yi maka zunubi, sa’ad da kuwa suka yi addu’a suna duban waje wannan wuri suka kuma furta sunanka suka juye daga zunubinsu domin ka azabta su,

27sai ka ji daga sama ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace da za su yi zama, ka kuma aika ruwan sama a ƙasar da ka ba mutanenka gādo.

28“Sa’ad da yunwa ko annoba ta fāɗo a ƙasar, ko wahala ko fumfuna, ko fāra ko fāra ɗango, ko sa’ad da abokan gāba sun yi musu ƙawanya a kowane daga biranensu, dukan wata masifa ko cutar da za tă zo,

29sa’ad da kuwa wani cikin mutanenka Isra’ila ya yi wata addu’a ko roƙo, kowa yana sane a azabarsa da kuma zafinsa, yana buɗe hannuwansa yana duban wajen wannan haikali,

30sai ka ji daga sama, mazauninka. Ka gafarta, ka kuma yi da kowane mutum gwargwadon duk abin da yake yi, da yake ka san zuciyarsa (gama kai kaɗai ka san zukatan mutane),

31don su ji tsoronka su kuma yi tafiya a hanyoyinka a kowane lokacin da suke zama a ƙasar da ka ba wa kakanninsu.

32“Game da baƙo wanda shi ba na mutanenka Isra’ila ba kuwa amma ya zo daga ƙasa mai nisa saboda sunanka mai girma da kuma hannunka mai iko da hannunka mai ƙarfi, sa’ad da ya zo ya yi addu’a yana duban wannan haikali,

33sai ka ji daga sama, mazauninka, ka kuma yi duk abin da baƙon ya nemi ka yi, saboda dukan mutanen duniya su san sunanka su kuma ji tsoronka, kamar yadda mutanenka Isra’ila suke yi, su kuma san cewa wannan gidan da na gina na Sunanka ne.

34“Sa’ad da mutanenka suka je yaƙi da abokan gābansu, ko’ina ka kai su, kuma sa’ad da suka yi addu’a gare ka suna duban wannan birnin da ka zaɓa da haikalin nan da na gina domin Sunanka,

35sai ka ji addu’arsu da kuma roƙonsu daga sama, ka kuma biya musu bukatarsu.

36“Sa’ad da suka yi maka zunubi, gama babu wani wanda ba ya zunubi, ka kuwa yi fushi da su ka miƙa su ga abokin gāba, wanda ya kai su zaman bauta a ƙasa mai nisa ko kuwa kusa;

37Kuma in suka canja zuciya a cikin ƙasar da suke zaman bauta, suka tuba suka roƙe ka a ƙasar zaman bautarsu suka kuma ce, ‘Mun yi zunubi, mu yi abin da ba daidai ba, mu kuwa yi mugunta’;

38in kuma sun juye gare ka da dukan zuciyarsu da ransu a ƙasar zaman bautarsu inda aka kai su, suka kuma dubi wajen ƙasar da ka ba wa kakanninsu, wajen birnin da ka zaɓa da kuma wajen haikalin da na gina domin Sunanka;

39to, daga sama, mazauninka, sai ka ji addu’arsu da kuma roƙe-roƙensu, ka kuwa biya musu bukatunsu. Ka gafarta wa mutanenka, waɗanda suka yi maka zunubi.

40“Yanzu, Allahna, bari idanunka su buɗu kunnuwanka kuma su saurara ga addu’o’in da ake miƙa a wannan wuri.

41“Yanzu ka tashi, ya Ubangiji Allah, ka zo wurin hutunka, kai da akwatin alkawarin ƙarfinka. Bari firistocinka, ya Ubangiji Allah, su sanye ceto, bari tsarkakanka su yi farin ciki cikin alherinka.

42Ya Ubangiji Allah, kada ka ƙyale shafaffenka. Ka tuna da ƙauna mai girma da ka alkawarta wa Dawuda bawanka.”

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY