Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Sarakunan Yahuda

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Sarakunan Yahuda

Ahaz sarkin Yahuda

2Sar 16:1–20 · 2Tar 28:1–27

2 Sarakuna

2Sar 16:1–20

1A shekara ta goma sha bakwai ta mulkin Feka ɗan Remaliya, Ahaz ɗan Yotam sarkin Yahuda ya fara mulki.

2Ahaz ya zama sarki yana da shekara ashirin, ya kuma yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima ba kamar Dawuda mahaifinsa ba. Ahaz bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa ba.

3Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila har ya miƙa ɗansa hadaya a wuta, yana bin hanyoyin banƙyama na al’ummai da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.

4Ya miƙa hadaya, ya kuma ƙona turare a masujadan tudu, da kan tuddai, da kuma a ƙarƙashin kowane babban itace.

5Sai Rezin sarkin Aram, da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su kai wa Urushalima hari, suka kuma kewaye Ahaz, amma ba su iya shan ƙarfinsa ba.

6A wannan lokaci, Rezin sarkin Aram ya sāke ƙwato Elat wa Aram ta wurin korar Yahuda. Sa’an nan mutanen Edom suka mamaye Elat suna kuwa zaune a can har yau.

7Ahaz ya aika a faɗa wa Tiglat-Fileser sarkin Assuriya cewa, “Ni abokin tarayyarka ne kuma mai dogara da kai. Ka haura ka cece ni daga hannun sarkin Aram da hannun sarkin Isra’ila waɗanda suke kawo mini hari.”

8Ahaz ya ɗauki azurfa da zinariyar da suke a haikalin Ubangiji da suke kuma a ma’ajin fada ya aika wa sarkin Assuriya kyauta.

9Sai sarkin Assuriya ya ji roƙonsa. Ya tashi ya fāɗa wa Damaskus da hari ya kuma kame ta. Ya kwashi mazaunanta zuwa Kir, ya kuma kashe Rezin.

10Sa’an nan sarki Ahaz ya tafi Damaskus don yă sadu da Tiglat-Fileser sarkin Assuriya. Da ya kai can sai ya ga wani bagade a Damaskus, sai ya aika wa Uriya firist, da siffar bagaden, da fasalinsa, da cikakken bayanin bagaden.

11Saboda haka Uriya firist ya gina bagaden bisa ga tsarin da Sarki Ahaz ya aika masa daga Damaskus, ya kuma gama shi kafin Sarki Ahaz yă dawo.

12Da sarki ya dawo daga Damaskus ya ga bagaden, sai ya tafi kusa da shi ya kuma miƙa hadaya a bisansa.

13Ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa da ta hatsi, ya zuba hadayarsa ta sha, ya kuma yayyafa jinin hadayunsa ta zumunci a bisa bagaden.

14Sai ya cire bagaden tagulla wanda aka keɓe ga Ubangiji, ya sa shi a gaban haikalin wato, tsakanin ƙofar shiga haikalin Ubangiji da sabon bagaden. Ya ajiye shi a gefen arewa na sabon bagaden.

15Sarkin Ahaz ya umarci Uriya cewa, “A kan babban sabon bagade, ka miƙa hadayar ƙonawa ta safe, da hadayar hatsi ta yamma, da hadayar sarki ta ƙonawa da hadayarsa ta hatsi, da hadaya ta dukan jama’ar ƙasar, tare da hadayan hatsinsu da kuma ta sha. Ka yayyafa jinin hadayun ƙonawa a kan bagade. Amma zan yi amfani da bagaden tagulla don neman bishewa.”

16Uriya firist kuwa ya yi duk abin da Sarki Ahaz ya umarta.

17Sarkin Ahaz ya kawar da katakon ya kuma ɗauke tasoshin daga mazauninsu da ake iya matsarwa. Ya ɗauke ƙaton kwano mai suna Teku daga kan bijiman tagullar da ya tallafe su ya ajiye a kan mazaunin dutse.

18Ya kawar da rumfa Asabbacin da aka gina a haikalin, ya kuma kawar da mashigin sarki na waje da haikalin Ubangiji, duk dai don yă gamshi sarkin Assuriya.

19Game da sauran ayyukan mulkin Ahaz, abubuwan da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.

20Ahaz ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi da su a Birnin Dawuda. Hezekiya ɗansa kuma ya gāje shi.

2 Tarihi

2Tar 28:1–27

1Ahaz yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Ba kamar Dawuda kakansa ba, bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji ba.

2Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila ya kuma yi zubin gumaka domin a bauta wa Ba’al.

3Ya ƙone hadayu a Kwarin Ben Hinnom, ya kuma miƙa ’ya’yansa maza a cikin wuta, yana bin hanyoyi banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.

4Ya miƙa hadayu, ya kuma ƙone turare a masujadan kan tudu, a bisa tuddai da kuma ƙarƙashin kowane itace mai inuwa.

5Saboda haka Ubangiji Allahnsa ya miƙa shi ga sarkin Aram. Arameyawa suka ci shi a yaƙi, suka kuma kwashe mutanensa da yawa a matsayin ’yan kurkuku, suka kawo Damaskus. Ya kuma ba da shi ga sarkin Isra’ila, wanda ya jijji masa a yaƙi.

6A rana ɗaya Feka ɗan Remaliya ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu ashirin a Yahuda, domin Yahuda sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu.

7Zikri, wani jarumin Efraim, ya kashe Ma’asehiya ɗan sarki, Azrikam hafsa mai lura da fada, da kuma Elkana, mataimakin sarki.

8Isra’ilawa suka kame kamammu daga ’yan’uwansu mata, ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata dubu ɗari biyu. Suka kuma kwashe ganima mai yawan gaske, waɗanda suka kwasa zuwa Samariya.

9Amma wani annabin Ubangiji mai suna Oded yana a can, sai ya fito don yă sadu da mayaƙa sa’ad da suke komowa zuwa Samariya. Ya ce musu, “Domin Ubangiji Allah na kakanninku yana fushi da Yahuda, ya ba da su cikin hannunku. Sai kuka kashe su cikin fushin da ya kai sama.

10Yanzu kuma kuna niyya ku mai da maza da matan Yahuda da Urushalima bayinku. Amma ku ɗin ba ku da laifin zunubi ga Ubangiji Allahnku ne?

11To, ku saurare ni! Ku mai da ’yan’uwanku da kuka kama a matsayin ’yan kurkuku, gama fushin Ubangiji yana a kanku.”

12Sai waɗansu shugabanni a Efraim, Azariya ɗan Yehohanan, Berekiya ɗan Meshillemot, Hezekiya ɗan Shallum da Amasa ɗan Hadlai, suka tasar wa waɗanda suke isowa daga yaƙi.

13Suka ce, “Dole ku kawo waɗannan ’yan kurkukun a nan, ko kuwa za ku yi laifi a gaban Ubangiji. Kuna niyya ku ƙara ga zunubinmu da kuma laifinmu? Gama laifinmu ya riga ya yi yawa, kuma fushinsa mai tsanani yana a kan Isra’ila.”

14Saboda haka sojoji suka ba da ’yan kurkukun da ganima a gaban hafsoshi da dukan taron.

15Sai mutanen da aka kira sunansu suka tashi, suka ɗauki kamammun, da ganimar, suka sa wa dukan waɗanda suke tsirara sutura. Suka sa musu sutura, suka ba su takalma, suka ba su abinci da abin sha, suka shafa musu mai. Suka hawar da dukan raunana a kan jakuna, suka kai su wurin ’yan’uwansu a Yeriko, wato, Birnin Itatuwan Dabino, sa’an nan suka koma Samariya.

16A lokacin nan Sarki Ahaz ya aika wurin sarkin Assuriya neman taimako.

17Mutanen Edom sun sāke zuwa suka yaƙi Yahuda suka kuma kwashe ’yan kurkuku,

18yayinda Filistiyawa suka kai hari wa garuruwa a gindin tuddai da kuma a Negeb na Yahuda. Suka kame su suka kuma zauna a Bet-Shemesh, Aiyalon da Gederot, haka ma Soko, Timna da Gimzo tare da ƙauyuka kewayensu.

19Ubangiji ya ƙasƙantar da Yahuda saboda Ahaz sarkin Isra’ila, gama ya hadasa mugunta a Yahuda kuma ya kasance marar aminci ga Ubangiji.

20Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya zo wurinsa, sai ya wahalar da sarki Ahaz maimakon taimakonsa.

21Ahaz ya ɗauki waɗansu abubuwa daga haikalin Ubangiji da kuma daga fadan sarki da kuma daga sarakuna, ya ba da su ga sarkin Assuriya, amma wannan bai taimake shi ba.

22Cikin lokacin wahalarsa Sarki Ahaz ya ƙara zama marar aminci ga Ubangiji.

23Ya miƙa hadayu ga allolin Damaskus, waɗanda suka ci shi a yaƙi; gama ya yi tunani, “Da yake allolin sarakunan Aram sun taimake su, zan miƙa hadayu domin su taimake ni.” Amma suka zama sanadin fāɗuwarsa da kuma fāɗuwar dukan Isra’ila.

24Ahaz ya tattara kayayyaki daga haikalin Allah ya kwashe su. Ya kulle ƙofofin haikalin Ubangiji ya kakkafa bagadai a kowace kusurwa a titin Urushalima.

25A kowane gari a Yahuda, ya gina masujadan kan tudu don ƙone hadayu ga waɗansu alloli, ya kuma tsokane Ubangiji Allah na kakanninsa ya yi fushi.

26Sauran ayyukan mulkinsa da dukan hanyoyinsa, daga farko zuwa ƙarshe, suna a rubuce a littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila.

27Ahaz ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Urushalima, amma ba a sa shi a makabartan sarakunan Isra’ila ba. Sai Hezekiya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY