Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Kariya

Lokutan wahala

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Kariya

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (10), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

K Mag 18:10Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi; masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.
Ish 54:17ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara, za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki. Wannan ne gādon bayin Ubangiji, kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,” in ji Ubangiji.
Ish 41:10Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai; kada ka karai, gama ni ne Allahnka. Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka; zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
Zab 46:1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce. Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
Zab 4:8Zan kwanta in kuma yi barci lafiya, gama kai kaɗai, ya Ubangiji, kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.
2Tes 3:3Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan.
Zab 32:7Kai ne wurin ɓuyata; za ka tsare ni daga wahala ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Sela
M Sh 31:6Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”
Zab 138:7Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala, kana kiyaye raina; ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana, da hannunka na dama ka cece ni.
Zab 34:7Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa, ya kuwa cece su.

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.