Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Ƙarfin hali

Lokutan wahala

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Ƙarfin hali

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (10), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

M Sh 31:6Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”
Yosh 1:9Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”
Zab 112:7Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba; zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.
2Tim 1:7Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.
K Mag 28:1Mugu yakan gudu ko babu wanda yake korarsa, amma adalai suna da ƙarfin hali kamar zaki.
Zab 31:24Ku yi ƙarfin hali ku kuma ƙarfafa, dukanku masu sa bege a kan Ubangiji.
1Kor 16:13Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.
Yoh 16:33“Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”
Zab 27:14Ka dogara ga Ubangiji, ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya ka kuma dogara ga Ubangiji.
Yosh 1:6“Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, gama kai za ka bi da mutanen nan har su karɓi ƙasar da na yi wa kakanninsu alkawari zan ba su.

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.