Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Maimaitawar Shari’a 18:10–12
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Maimaitawar Shari’a 18:10–12
10Kada a sami wani a cikinku da ya miƙa ɗansa, ko ’yarsa a wuta, ko a sami mai duba, ko mai maita, ko mai fassara gaibi, ko mai sihiri,
11ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha’ani da matattu.
12Duk wanda yake yin waɗannan abubuwa, shi abin ƙyama ne ga Ubangiji, saboda waɗannan abubuwa banƙyama ne kuwa Ubangiji Allahnku ya kori waɗancan al’ummai kafin ku.
Karanta dukan babin: Maimaitawar Shari’a 18
A cikin mahallinsa
7Zai iya yin hidima a cikin sunan Ubangiji Allahnsa kamar dukan sauran ’yan’uwansa Lawiyawa waɗanda suke hidima a can, a gaban Ubangiji.
8Zai sami rabo daidai da sauran, ko da yake ya karɓi kuɗin mallaka na iyali da ya sayar.
9Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku kwaikwayi hanyoyin banƙyama na al’ummai da suke can.
10Kada a sami wani a cikinku da ya miƙa ɗansa, ko ’yarsa a wuta, ko a sami mai duba, ko mai maita, ko mai fassara gaibi, ko mai sihiri,
11ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha’ani da matattu.
12Duk wanda yake yin waɗannan abubuwa, shi abin ƙyama ne ga Ubangiji, saboda waɗannan abubuwa banƙyama ne kuwa Ubangiji Allahnku ya kori waɗancan al’ummai kafin ku.
13Dole ku zama marasa zargi a gaban Ubangiji Allahnku.
14Al’ummai da za ku kora sukan saurari waɗannan masu maita, ko masu duba. Amma ku, Ubangiji Allahnku bai yarda muku ku yi haka ba.
15Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamar ni daga cikin ’yan’uwanku. Dole ku saurare shi.
Da Turanci
Let no one be found among you who sacrifices his son or daughter in the fire, practices divination or conjury, interprets omens, practices sorcery, casts spells, consults a medium or spiritist, or inquires of the dead. For whoever does these things is detestable to the LORD. And because of these detestable things, the LORD your God is driving out the nations before you.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
“ ‘Kada ku juya ga masu duba, ko ku nemi shawarar bokaye, gama za ku ƙazantu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji Allahnku.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi