Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2027 › Disamba 14

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Disamba 14, 2027

Talata · Mako na 3 na lokacin Zuwan Ubangiji

Bukukuwa da waliyyai

Talata a mako na 3 na lokacin Zuwan Ubangiji

Tunawa · Launin ibada: fari

Waliyyi John na Gicciye, firist kuma malamin Ikkilisiya · Tunawa

Karatun yini

Karatu na farko

Zef 3:1–2, 9–13

1Taki ta ƙare, ke birnin mai danniya, mai ’yan tawaye da kuma masu ƙazanta! 2Ba kya yi wa kowa biyayya, ba kya kuma yarda da kuskurenki. Ba kya dogara ga Ubangiji, ba kya kuma kusatowa kusa da Allahnki. 9“Sa’an nan zan tsarkake leɓunan mutanen, don dukansu su kira bisa ga sunan Ubangiji su kuma yi masa hidima kafaɗa da kafaɗa. 10Tun daga ƙetaren rafuffukan Kush masu yi mini sujada, mutanena da suke a warwatse, za su kawo mini hadayu. 11A wannan rana ba za ku sha kunya saboda laifofin da kuka yi mini, gama zan ɗauke wa wannan birni waɗanda suke farin ciki cikin girmankansu. Ba kuma za ka ƙara yin kallon reni a tuduna mai tsarki ba. 12Amma zan zauna a cikinki masu tawali’u da masu ƙasƙantar da kai, waɗanda suke dogara ga sunan Ubangiji. 13Raguwar Isra’ila ba za su ƙara aikata abin da ba daidai ba, ba za su faɗa ƙarya ba, ba kuwa za a sami ruɗu a bakunansu ba. Za su ci su kuma kwanta kuma babu wanda zai ba su tsoro.”

Zaburar amsawa

Zab 34:1–2, 5–6, 16–18, 22

1Ta Dawuda. Sa’ad da ya yi kamar ya haukace a gaban Abimelek, Wanda ya kore shi, ya kuwa tafi. Zan gode wa Ubangiji kullayaumi; yabonsa kullum za su kasance a leɓunana. 2Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji; bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki. 5Waɗanda suke dubansa sukan haskaka; fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya. 6Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi; ya cece shi daga dukan wahalarsa. 16fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta, don yă sa a manta da su a duniya. 17Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su; yakan cece su daga dukan wahalarsu. 18Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu. 22Ubangiji yakan cece bayinsa; ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.

Bishara

Mat 21:28–32

28“Me kuka gani? An yi wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. Sai ya je wajen ɗan farin ya ce, ‘Ɗana, yau tafi gonar inabi ka yi aiki.’ 29“Ya amsa ya ce, ‘Ba zan tafi ba,’ amma daga baya ya sāke tunani, ya tafi. 30“Sai mahaifin ya tafi waje na biyun ya faɗa masa iri magana guda. Sai ya amsa ya ce, ‘Zan tafi, ranka yă daɗe,’ amma bai tafi ba. 31“Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?” Suka amsa, “Na farin.” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah. 32Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo wurinku don yă nuna muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba, amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata. Har ma bayan kun ga wannan, ba ku tuba kun gaskata shi ba.”

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi C, shekarar ranakun mako II.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi