Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Nuwamba 2027 › Nuwamba 4
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Nuwamba 4, 2027
Alhamis · Mako na 31 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Alhamis a mako na 31 na lokacin yau da kullum
Tunawa · Launin ibada: fari
Waliyyi Charles Borromeo, bishop · Tunawa
Karatun yini
Karatu na farko
7Gama ba waninmu da yake rayuwa wa kansa kaɗai, kuma ba waninmu da kan mutu don kansa kaɗai. 8In muna rayuwa, muna rayuwa ne ga Ubangiji; in kuma muna mutuwa, muna mutuwa ne ga Ubangiji. Saboda haka, ko muna a raye ko muna a mace, mu na Ubangiji ne. 9Saboda wannan ne Kiristi ya mutu, ya kuma sāke rayuwa domin yă zama Ubangiji na matattu da na masu rai. 10Kai kuwa, don me kake ganin laifin ɗan’uwanka? Ko kuma don me kake rena ɗan’uwanka? Gama duk za mu tsaya a gaban kujerar shari’ar Allah. 11A rubuce yake cewa, “ ‘Muddin ina raye,’ in ji Ubangiji, ‘kowace gwiwa za tă durƙusa a gabana; kowane harshe kuma zai furta wa Allah.’ ” 12Don haka kowannenmu zai ba da lissafin kansa ga Allah.
Zaburar amsawa
1Ta Dawuda. Ubangiji ne haskena da cetona, wa zan ji tsoro? Ubangiji ne mafakar raina, wane ne zan ji tsoro? 4Abu guda na roƙi Ubangiji, wannan shi ne na nema, cewa in zauna a gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, in dubi kyan Ubangiji in kuma neme shi a cikin haikalinsa. 13Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa zan ga alherin Ubangiji; a ƙasar masu rai. 14Ka dogara ga Ubangiji, ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya ka kuma dogara ga Ubangiji.
Bishara
1Yanzu fa, masu karɓar haraji da “masu zunubi” duka suna taruwa don jin koyarwar Yesu. 2Amma Farisiyawa da malaman dokoki suka yi gunaguni, suna cewa, “Wannan mutum yana karɓan ‘masu zunubi,’ kuma yana ci tare da su.” 3Sai Yesu ya faɗa musu wannan misali ya ce, 4“In ɗayanku yana da tumaki ɗari, sa’an nan ɗayansu ta ɓace. Ashe, ba zai bar tasa’in da tara a fili ya je neman wadda ta ɓace, har sai ya same ta ba? 5In ya same ta, zai sa ta a kafaɗa da murna, 6ya dawo gida. Sa’an nan zai kira abokansa da maƙwabtansa wuri ɗaya ya ce, ‘Ku taya ni murna, na sami tunkiyana da ta ɓata.’ 7Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasa’in da tara, waɗanda ba su bukatan tuba. 8“Ko kuwa in wata mace tana da kuɗi na azurfa guda goma, sa’an nan ɗaya ya ɓata, ashe, ba za tă ƙuna fitila, ta share gidan, ta nema a hankali, har sai ta samu ba? 9In ta same shi, sai ta kira ƙawayenta da maƙwabtanta wuri ɗaya, ta ce musu, ‘Ku taya ni murna, na sami kuɗina da ya ɓata.’ 10Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban mala’ikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba.”
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Charles Borromeo, bishop
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi