Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2027 › Oktoba 16
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Oktoba 16, 2027
Asabar · Mako na 28 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Asabar a mako na 28 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Waliyya Hedwig, mai zuhudu · Tunawa da ba dole ba
Waliyya Margaret Mary Alacoque, budurwa · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
13Ba ta wurin doka ce Ibrahim da zuriyarsa suka sami alkawarin cewa zai zama magājin duniya ba, amma sai dai ta wurin adalcin da yake zuwa ta wurin bangaskiya. 16Saboda haka, alkawari yakan zo ta wurin bangaskiya ne, domin yă zama ta wurin alheri, don a tabbatar wa dukan zuriyar Ibrahim ba kawai ga waɗanda suke na doka ba amma har ma ga waɗanda suke na bangaskiyar Ibrahim. Shi ne kuwa mahaifinmu duka. 17Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na mai da kai uban al’ummai masu yawa.” Shi ubanmu ne a gaban Allah, wanda a cikinsa ya gaskata, Allahn da yake ba da rai ga matattu, yake kuma kiran abubuwan da ba su kasance ba su zama kamar sun kasance. 18Saɓanin dukan bege, Ibrahim cikin bege ya gaskata, haka kuwa ya zama uban al’ummai masu yawa, kamar yadda aka riga aka faɗa masa cewa, “Haka zuriyarka za tă zama.”
Zaburar amsawa
6Ya ku zuriyar Ibrahim bawansa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub, zaɓaɓɓensa. 7Shi ne Ubangiji Allahnmu; kuma hukunce-hukuncensa suna a cikin dukan duniya. 8Yana tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu, 9alkawarin da ya yi da Ibrahim, rantsuwar da ya yi wa Ishaku. 42Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki da ya ba wa bawansa Ibrahim. 43Ya fitar da mutanensa da farin ciki, zaɓaɓɓunsa da sowa ta farin ciki;
Bishara
8“Ina gaya muku, duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai shaida shi a gaban mala’ikun Allah. 9Amma wanda ya yi mūsun sanina a gaban mutane, shi ma za a yi mūsunsa a gaban mala’ikun Allah. 10Kuma duk wanda ya faɗi kalmar zagi a kan Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya saɓa wa Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba. 11“Sa’ad da an kai ku a gaban majami’u, da gaban masu mulki, da kuma gaban masu iko, kada ku damu da yadda za ku kāre kanku, ko kuma abin da za ku faɗa, 12gama Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya dace ku faɗa a lokacin.”
Tsarkakan ranar
- Waliyya Hedwig, mai zuhudu
- Waliyya Margaret Mary Alacoque, budurwa
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi