Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Satumba 2027 › Satumba 17
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Satumba 17, 2027
Juma’a · Mako na 24 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Juma’a a mako na 24 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Waliyya Hildegard ta Bingen, budurwa kuma malamar Ikkilisiya · Tunawa da ba dole ba
Waliyyi Robert Bellarmine, bishop kuma malamin Ikkilisiya · Tunawa da ba dole ba
Azumi da tuba
Ranar tuba
Kowace Juma’a ranar tuba ce; kowace taron bishop-bishop yana tsara yadda ake kiyaye ta: kamewa daga nama ko wani aikin tuba. Azumi ya wajaba daga shekara 18 zuwa 59, kamewa daga shekara 14.
Karatun yini
Karatu na farko
2Waɗanda suke da iyayengiji masu bi, to, kada su yi musu reni domin su ’yan’uwa ne. A maimako, sai ma su fi bauta musu, saboda waɗanda suke cin moriyar hidimarsu masu bi ne, ƙaunatattu ne kuma a gare su. Waɗannan su ne abubuwan da za ka koya musu ka kuma gargaɗe su. 3In wani yana koyarwar ƙarya bai kuma yarda da sahihiyar koyarwar Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma koyarwa ta tsoron Allah ba, 4yana cike da girman kai bai kuma san kome ba. Yana da mugun halin son gardama da muhawwara game da kalmomin da suke kawo kishi, rikici, maganar ƙeta, da mugayen zace-zace 5da yawan tankiya tsakanin mutane masu mugun hali, waɗanda aka raba su da gaskiya, suke kuma tsammani cewa bin Allah wata hanya ce ta samun kuɗi. 6Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa. 7Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. 8In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su. 9Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. 10Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri. 11Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali. 12Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa.
Zaburar amsawa
5Don me zan ji tsoro sa’ad da mugayen kwanaki suka zo, sa’ad da mugaye masu ruɗu suka kewaye ni, 6waɗanda suka dogara ga arzikinsu suna kuma fariya a kan yawan arzikinsu? 7Ba wani da zai iya ceton ran wani ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi, 8kuɗin fansa domin rai yana da tsada, babu abin da za a biya da ya taɓa isa, 9da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada yă hana shi shigan kabari yă ruɓa. 16Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki sa’ad da darajar gidansa ta ƙaru; 17gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba, darajarsa ba za tă gangara tare da shi ba. 18Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne, mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara, 19zai gamu da tsarar kakanninsa, waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba.
Bishara
1Bayan wannan sai Yesu ya zazzaga gari da ƙauye, yana wa’azin bisharar mulkin Allah. Sha Biyun nan kuwa suna tare da shi, 2da kuma waɗansu mata waɗanda aka warkar da su daga cututtukansu, da kuma mugayen ruhohi. Cikinsu akwai Maryamu (wadda ake kira Magdalin) wadda aljanu bakwai suka fito daga cikinta. 3Da Yowanna matar Kuza, manajan iyalin Hiridus; da Suzana; da waɗansu mata da yawa. Waɗannan mata suna taimaka musu cikin hidima, daga cikin abin da suke da shi na zaman gari.
Tsarkakan ranar
- Waliyya Hildegard ta Bingen, budurwa kuma malamar Ikkilisiya
- Waliyyi Robert Bellarmine, bishop kuma malamin Ikkilisiya
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi