Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Satumba 2027 › Satumba 4
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Satumba 4, 2027
Asabar · Mako na 22 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Asabar a mako na 22 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Tunawa da Budurwa Maryamu Mai Albarka a ranar Asabar · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
21A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku. 22Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi. 23Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta.
Zaburar amsawa
1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Zifawa suka tafi wurin Shawulu suka ce, “Ba Dawuda ba ne yake ɓuya a cikinmu?” Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka; ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka. 2Ka ji addu’ata, ya Allah; ka saurari maganar bakina. 4Tabbatacce Allah ne mai taimakona, Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni. 6Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka; zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau.
Bishara
1A wata ranar Asabbaci, Yesu yana bi ta gonakin hatsi, sai almajiran suka fara kakkarya kan hatsi suna murjewa a hannuwansu suna ci. 2Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Me ya sa kuke yin abin da doka ta hana yi a ranar Asabbaci?” 3Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi, sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa ba? 4Ya shiga gidan Allah, ya ɗauki keɓaɓɓen burodi, sa’an nan ya ci abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka. Ya kuma ba wa abokan tafiyarsa?” 5Sai Yesu ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum ne Ubangijin Asabbaci.”
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi