Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Yuni 2027 › Yuni 1

Kalandar Ortodoks · 19 ga Mayu (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Yuni 1, 2027

Talata · Mako na 5 na lokacin Ista · Sauti na 4

Bukukuwa da waliyyai

Hieromartyrs Patrick the Bishop of Prussa and the Priests Acacius, Menander, and Polyenus († c. 100)

Azumi

Babu azumi

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Wasiƙa

Ayy M 12:25–13:12

25Sa’ad da Barnabas da Shawulu suka kammala aikinsu, sai suka komo daga Urushalima, tare da Yohanna, wanda ake kira Markus. 13:1A ikkilisiyar da take a Antiyok akwai waɗansu annabawa da malamai. Barnabas, Siman wanda ake kira Baƙi, Lusiyus mutumin Sairin, Manayen (wanda aka goya tare da Hiridus mai mulki), da kuma Shawulu. 2Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawulu domin aikin da na kira su.” 3Saboda haka bayan suka yi azumi da addu’a, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su. 4Sai su biyu da Ruhu Mai Tsarki ya aika suka gangara zuwa Selusiya suka shiga jirgin ruwa daga can zuwa Saifurus. 5Da suka isa Salamis, sai suka yi shelar maganar Allah a majami’un Yahudawa. Yohanna yana tare da su a matsayin mai taimakonsu. 6Suka zaga dukan tsibirin har sai da suka kai Bafos. A can suka sadu da wani mutumin Yahuda mai sihiri, annabin ƙarya, mai suna Bar-Yesu, 7wanda yake ma’aikacin muƙaddas Sergiyus Bulus ne. Muƙaddas ɗin kuwa mai azanci ne ƙwarai, ya sa aka kira Barnabas da Shawulu don yana so ya ji maganar Allah. 8Amma Elimas mai sihirin nan (domin ma’anar sunansa ke nan) ya yi hamayya da maganarsu ya kuma yi ƙoƙari ya juyar da muƙaddas ɗin daga bangaskiya. 9Sai Shawulu, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya kafa wa Elimas ido ya ce, 10“Kai ɗan Iblis ne abokin gāban dukan abin da yake daidai! Kana cike da kowane irin ruɗi da munafunci. Ba za ka daina karkata hanyoyin da suke daidai na Ubangiji ba? 11Ga shi hannun Ubangiji yana gāba da kai. Za ka makance, kuma ba za ka ga rana ba har na wani lokaci.” Nan take, hazo da duhu suka sauko a kansa, ya yi ta lallubawa, yana neman wanda zai yi masa jagora. 12Sa’ad da muƙaddas ɗin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, gama ya yi mamaki a kan da koyarwa game Ubangiji.

Bishara

Yoh 8:51–59

51Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya kiyaye maganata, ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.” 52Da jin haka Yahudawa suka ce, “Tabɗi, yanzu kam mun san kana da aljani! Ibrahim ya mutu haka ma annabawa, ga shi kana cewa duk wanda ya kiyaye maganarka ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam. 53Ka fi Ibrahim mahaifinmu ne? Ya mutu, haka ma annabawa. Wa kake ɗauka kanka ne?” 54Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba kome ba ce. Ubana, wanda kuke cewa shi ne Allahnku, shi ne wanda yake ɗaukaka ni. 55Ko da yake ba ku san shi ba, ni dai na san shi. In kuwa na ce ban san shi ba, na zama maƙaryaci kamar ku ke nan, amma na san shi, kuma ina kiyaye maganarsa. 56Mahaifinku Ibrahim ya yi farin ciki sosai yă sami ganin ranata; ya kuwa gan ta, ya yi murna.” 57Sai Yahudawa suka ce masa, “Kai, shekarunka har yanzu ba su kai hamsin tukuna ba fa, har ka ga Ibrahim!” 58Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne!” 59Da jin haka sai suka ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, amma Yesu ya ɓuya, ya fita daga filin haikali.

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Mayu 19 a kalandar ikilisiya shi ne Yuni 1 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi