Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Mayu 2027 › Mayu 18
Kalandar Ortodoks · 5 ga Mayu (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Mayu 18, 2027
Talata · Mako na 3 na lokacin Ista · Sauti na 2
Bukukuwa da waliyyai
Great Martyr Irene of Thessalonica (1st-2nd C)
Azumi
Babu azumi
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Wasiƙa
5Filibus ya gangara zuwa wani birni a Samariya ya kuma yi shelar Kiristi a can. 6Sa’ad da taron mutane suka ji Filibus suka kuma ga abubuwan banmamakin da ya yi, sai duk suka mai da hankali sosai ga abin da ya faɗa. 7Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa. 8Saboda haka aka yi farin ciki ƙwarai a birnin. 9To, akwai wani mutum mai suna Siman wanda ya kwana biyu yana yin sihiri a birnin har ya ba wa duk mutanen Samariya mamaki. Ya kuma yi taƙama cewa shi wani mai girma ne, 10dukan mutane kuwa, manyan da ƙanana, suka mai da hankali gare shi suka kuma ce, “Mutumin nan shi ne ikon Allah da aka sani a matsayin Iko Mai Girma” 11Suka bi shi domin ya daɗe yana ba su mamaki da sihirinsa. 12Amma da suka gaskata da Filibus sa’ad da yake wa’azin labari mai daɗi na mulkin Allah da kuma sunan Yesu Kiristi, sai aka yi musu baftisma, maza da mata. 13Siman kansa ya gaskata aka kuma yi masa baftisma. Ya kuma bi Filibus ko’ina, yana mamakin manyan alamu da ayyukan banmamakin da ya gani. 14Sa’ad da manzannin da suke a Urushalima suka ji cewa Samariya ta karɓi maganar Allah, sai suka aika musu da Bitrus da Yohanna. 15Da suka iso, sai suka yi musu addu’a domin su karɓi Ruhu Mai Tsarki, 16domin Ruhu Mai Tsarki bai riga ya sauka wa waninsu ba tukuna, an dai yi musu baftisma ne kawai a cikin sunan Ubangiji Yesu. 17Sa’an nan Bitrus da Yohanna suka ɗibiya hannuwansu a kansu, suka kuwa karɓi Ruhu Mai Tsarki.
Bishara
27Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yă zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.” 28Sai suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi don mu aikata ayyukan da Allah yake so?” 29Yesu ya amsa, “Aikin Allah shi ne, a gaskata da wanda ya aiko.” 30Sai suka tambaye shi, “Wace abin banmamaki ce za ka yi don mu gani mu kuwa gaskata ka? Me za ka yi? 31Kakannin-kakanninmu sun ci Manna a hamada; kamar yadda yake a rubuce, ‘Ya ba su burodi daga sama su ci.’” 32Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba Musa ne ya ba ku burodi daga sama ba, sai dai Ubana ne yake ba ku burodi na gaskiya daga sama. 33Gama burodin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama, yana kuma ba wa duniya rai.”
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Mayu 5 a kalandar ikilisiya shi ne Mayu 18 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi