Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Afirilu 2027 › Afirilu 11

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Afirilu 11, 2027

Lahadi · Mako na 3 na lokacin Ista

Bukukuwa da waliyyai

Lahadi ta 3 ta lokacin Ista

Lahadi · Launin ibada: fari

Karatun yini

Karatu na farko

Ayy M 3:13–15, 17–19

13Allah na Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub, Allah na kakanninmu, ya ɗaukaka bawansa Yesu. Ku kuka ba da shi domin a kashe, kuka yi mūsun saninsa a gaban Bilatus, ko da yake ya yi niyya ya sake shi. 14Kuka yi mūsun sanin Mai Tsarki da Mai Adalci kuka roƙa a sakar muku mai kisankai. 15Kuka kashe tushen rai, amma Allah ya tashe shi daga matattu. Mu shaidu ne ga wannan. 17“To, ’yan’uwa, na san cewa, kun aikata wannan cikin jahilci ne, yadda shugabanninku suka yi. 18Amma ta haka ne Allah ya cika abin da ya rigyafaɗi ta bakin dukan annabawa cewa, Kiristinsa zai sha wahala. 19Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji,

Zaburar amsawa

Zab 4:1, 6, 8

1Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda. Ka amsa mini sa’ad da na kira gare ka, Ya Allahna mai adalci. Ka ba ni sauƙi daga wahalata; ka ji tausayina ka kuma ji addu’ata. 6Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?” Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji. 8Zan kwanta in kuma yi barci lafiya, gama kai kaɗai, ya Ubangiji, kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.

Karatu na biyu

1Yoh 2:1–5

1’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci. 2Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka. 3Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa. 4Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa.

Bishara

Luk 24:35–48

35Sai su biyun nan suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane Yesu yayinda ya kakkarya burodin. 36Suna cikin wannan zance, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu. Sai ya ce musu, “Salama a gare ku!” 37Suka firgita, suka tsorota, suna tsammani fatalwa ce suka gani. 38Sai ya ce musu, “Don me kuke damuwa, kuke kuma shakka a zuciyarku? 39Ku duba hannuwana da ƙafafuna. Ai, ni ne da kaina! Ku taɓa ni ku ji, ai, fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.” 40Da ya faɗi haka, sai ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa. 41Kuma har yanzu, suna cikin rashin gaskatawa, saboda murna da mamaki, sai ya tambaye su, “Kuna da abinci a nan?” 42Suka ba shi ɗan gasasshen kifi, 43ya karɓa ya ci a gabansu. 44Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.” 45Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi. 46Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu. 47Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima. 48Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi