Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Oktoba 2026 › Oktoba 13

Kalandar Ortodoks · 30 ga Satumba (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Oktoba 13, 2026

Talata · Mako na 20 bayan Fentekos · Sauti na 2

Bukukuwa da waliyyai

Hieromartyr Gregory, Bishop and Enlightener of Great Armenia († c. 335)

Azumi

Babu azumi

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Wasiƙa

Fil 2:16–23

16kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba. 17Amma ko da ana tsiyaye jinina kamar hadaya ta sha a kan hadaya da kuma hidimar da take fitowa daga bangaskiyarku, ina murna ina kuma farin ciki da ku duka. 18Haka ma ya kamata ku yi murna ku kuma yi farin ciki tare da ni. 19Ina sa rai a cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika da Timoti zuwa gare ku ba da daɗewa ba, don ni ma in ji daɗi sa’ad da na ji labarinku. 20Ba ni da wani kamar sa, wanda yake da ainihin sha’awa a zaman lafiyarku. 21Gama kowa yana lura da al’amuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba. 22Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa. 23Saboda haka, ina sa rai, in aike shi da zarar na ga yadda abubuwa suke a nan.

Wasiƙa (domin Laraba)

Fil 2:24–30

24Ni kuma ina da tabbaci a cikin Ubangiji cewa zan zo ba da daɗewa ba. 25Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗan’uwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin yă biya mini bukatuna. 26Gama yana marmarin ganinku duka ya kuma damu domin kun ji cewa ya yi rashin lafiya. 27Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yă rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki. 28Saboda haka na yi niyya ƙwarai in aike shi wurinku, don sa’ad da kuka sāke ganinsa za ku yi murna, ni kuma in rage damuwa. 29Ku marabce shi cikin Ubangiji da farin ciki mai yawa, ku kuma girmama mutane irinsa, 30domin ya kusa yă mutu saboda aikin Kiristi, ya yi kasai da ransa don yă cikasa taimakon da ba ku iya yi mini ba.

Bishara

Luk 5:12–16

12Yayinda Yesu yake ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa. Da ganin Yesu, sai ya fāɗi da fuskarsa a ƙasa, ya roƙe shi ya ce, “Ubangiji, in ka yarda, kana iya ka tsabtacce ni.” 13Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka zama da tsabta!” Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi. 14Sai Yesu ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayu da Musa ya umarta, saboda tsarkakewarka ta zama shaida a gare su.” 15Duk da haka, labarinsa ya ƙara bazuwa sosai, har taron mutane suka dinga zuwa don jinsa, da kuma neman warkarwa daga cututtukansu. 16Amma Yesu sau da yawa, yakan keɓe kansa zuwa wuraren da ba kowa, yă yi addu’a.

Bishara (domin Laraba)

Luk 5:33–39

33Suka ce masa, “Almajiran Yohanna sukan yi azumi da addu’a, haka ma almajiran Farisiyawa, amma naka sai ci da sha.” 34Yesu ya amsa ya ce, “Za ku iya sa abokan ango yin azumi yayinda yake tare da su? 35Amma lokaci yana zuwa, da za a ɗauke ango daga gare su. A waɗancan kwanakin ne za su yi azumi.” 36Sai ya faɗa musu wannan misali ya ce, “Ba wanda yakan yage ƙyalle daga sabuwar riga ya yi wa tsohuwar riga faci. In ya yi haka, zai yage sabuwar rigar, kuma facin daga sabuwar ba zai dace da tsohuwar rigar ba. 37Kuma ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In ya yi haka, sabon ruwan inabi zai farfashe salkunan, ruwan inabin yă zube, salkunan kuma su lalace. 38A’a, sai dai a zuba sabon ruwan inabi a sababbin salkuna. 39Kuma ba wanda yakan so shan sabon ruwan inabi bayan ya sha tsohon, don yakan ce, ‘Ai, tsohon ya fi kyau.’ ”

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Satumba 30 a kalandar ikilisiya shi ne Oktoba 13 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi