Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Sarakunan Yahuda

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Sarakunan Yahuda

Mikahiya ya gargaɗi Ahab

1Sar 22:1–35 · 2Tar 18:1–34

1 Sarakuna

1Sar 22:1–35

1Aka yi shekaru uku ba a yi yaƙi tsakanin Aram da Isra’ila ba.

2Amma a shekara ta uku, Yehoshafat sarkin Yahuda ya gangara don yă ga sarki Isra’ila.

3Sarkin Isra’ila ya ce wa shugabanninsa, “Ba ku san cewa Ramot Gileyad namu ne ba, duk da haka ba mu yi kome ba don mu sāke karɓanta daga sarkin Aram?”

4Saboda haka ya tambayi Yehoshafat, ya ce, “Za ka tafi tare da ni don in yi yaƙi da Ramot Gileyad?” Yehoshafat ya amsa wa sarkin Isra’ila, ya ce, “Ni ma kamar ka ne, mutanena kuwa kamar mutanenka, dawakaina kamar dawakanka.”

5Amma Yehoshafat ya ce wa sarkin Isra’ila, “Da farko mu nemi nufin Ubangiji.”

6Saboda haka sarkin Isra’ila ya tattara annabawa, kamar ɗari huɗu, ya tambaye su, “In kai yaƙi a kan Ramot Gileyad, ko kada in kai?” Suka amsa, “Ka tafi, gama Ubangiji zai ba ka ita a hannunka.”

7Amma Yehoshafat ya yi tambaya, ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu tambaya?”

8Sarkin Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, ya ce, “Akwai mutum guda har yanzu wanda ta wurinsa za mu iya nemi nufin Ubangiji, amma na ƙi jininsa domin bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni ba, sai dai mummuna kullum. Shi ne Mikahiya ɗan Imla.” Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya ce haka.”

9Saboda haka sarkin Isra’ila ya kira ɗaya daga cikin shugabanninsa ya ce, “Kawo Mikahiya ɗan Imla nan take.”

10Saye da rigunansu na sarauta, sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suna zama a kujerun sarautarsu a masussuka ta mashigin ƙofar Samariya, tare da dukan annabawa suna ta annabci a gabansu.

11Zedekiya ɗan Kena’ana kuwa ya yi ƙahonin ƙarfe ya kuma furta, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan za ka tunkuyi Arameyawa har su hallaka.’ ”

12Dukan sauran annabawan suka yi annabci iri abu ɗaya. Suka ce, “Ka yaƙi Ramot Gileyad, ka kuma yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita cikin hannun sarki.”

13Ɗan aikan da ya je yă kawo Mikahiya, ya ce masa, “Duba, sauran annabawa suna maganar nasara wa sarki, sai ka ce mutum guda. Bari maganarka tă yarda da tasu, ka kuma yi maganar alheri.”

14Amma Mikahiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji mai rai, zan faɗa masa kawai abin da Ubangiji ya faɗa mini.”

15Da suka kai, sai sarki ya tambaye shi, ya ce, “Mikahiya, mu kai yaƙi a kan Ramot Gileyad, ko kada mu kai?” Ya amsa ya ce, “Yaƙe ta, za ka kuwa yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita cikin hannun sarki.”

16Sai sarki ya ce masa, “Sau nawa ne zan sa ka rantse cewa ba za ka faɗa mini kome ba sai dai gaskiya a cikin sunan Ubangiji?”

17Sa’an nan Mikahiya ya amsa, “Na ga dukan Isra’ila a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, kuma Ubangiji ya ce, ‘Waɗannan mutane ba su da maigida. Bari kowa yă tafi gida cikin salama.’ ”

18Sai sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka cewa bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni, sai mummuna kawai ba?”

19Mikahiya ya ci gaba, “Saboda haka ka ji maganar Ubangiji. I, na ga Ubangiji zaune a kursiyinsa tare da dukan rundunar sama tsaye kewaye da shi a dama da hagunsa.

20Kuma Ubangiji ya ce, ‘Wa zai ruɗi Ahab zuwa yaƙi da Ramot Gileyad, yă kuma kai shi mutuwarsa a can?’ “Wani ya ce wannan, wani ya ce wancan.

21A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’

22“Ubangiji ya yi tambaya ‘Ta wace hanya?’ Ya ce, “ ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’ “Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’

23“Saboda haka yanzu Ubangiji ya sa ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawanka. Ubangiji ya zartar maka da masifa.”

24Sai Zedekiya ɗan Kena’ana ya hau ya mari Mikahiya a fuska. Ya yi tambaya, “A wace hanya ce ruhu daga Ubangiji ya bar ni ya yi maka magana?”

25Mikahiya ya amsa, “Za ka gane a ranar da ka je ka ɓuya a ciki cikin ɗaki.”

26Sa’an nan sarkin Isra’ila ya umarta, “Ku kama Mikahiya, ku kai shi wurin Amon, shugaban birnin, da wurin Yowash ɗan sarki.

27Ku ce ga abin da sarki ya ce, ‘Ku sa wannan mutum a kurkuku, kuma kada ku ba shi wani abu sai dai burodi da ruwa, sai na dawo lafiya.’ ”

28Mikahiya ya furta, “Idan har ka dawo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana ta wurina ba.” Ya kuma ƙara da cewa, “Ku lura da maganata, dukanku mutane!”

29Sai sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suka haura zuwa Ramot Gileyad.

30Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Zan ɓad da kama in shiga wurin yaƙi, amma ka sa kayan sarautarka.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya ɓad da kama, ya shiga cikin yaƙi.

31Sarkin Aram kuwa ya umarci shugabanni kekunan yaƙinsa talatin da biyu, ya ce, “Kada ku yaƙe kowa, ƙarami ko babba, sai dai sarkin Isra’ila.”

32Sa’ad da shugabannin kekunan yaƙin suka ga Yehoshafat, suka yi tsammani, suka ce, “Tabbatacce wannan shi ne sarkin Isra’ila.” Saboda haka suka juye don su yaƙe shi, amma sa’ad da Yehoshafat ya yi ihu,

33sai shugabannin kekunan yaƙin suka ga ashe ba sarkin Isra’ila ba ne, sai suka daina binsa.

34Amma wani ya ja bakansa kawai ya bugi Ahab sarkin Isra’ila a tsakanin sassan kayan yaƙinsa. Sai sarki ya ce wa mahayin keken yaƙinsa, “Juye, ka fitar da ni daga yaƙin. An ji mini rauni.”

35Dukan yini aka yi ta yaƙi, aka kuma riƙe sarki a keken yaƙinsa yana fuskanci Arameyawa. Jini daga mikinsa ya yi ta zuba a ƙasan keken yaƙin, a wannan yamma kuwa ya mutu.

2 Tarihi

2Tar 18:1–34

1Yanzu fa Yehoshafat ya wadace ƙwarai yana kuma da girma, ya kuma haɗa kansa da Ahab ta wurin aure.

2Bayan ’yan shekaru sai ya gangara don yă ziyarci Ahab a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki da shanu masu yawa dominsa da kuma mutanen da suke tare da shi, ya kuma lallashe shi yă yaƙi Ramot Gileyad.

3Ahab sarkin Isra’ila ya tambayi Yehoshafat sarkin Yahuda ya ce, “Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Ramot Gileyad?” Yehoshafat ya amsa ya ce, “Ni kamar kai ne, kuma mutanena kamar naka ne; za mu tafi tare da kai a yaƙin.”

4Amma Yehoshafat ya kuma ce wa sarkin Isra’ila, “Da fari mu nemi bishewar Ubangiji.”

5Saboda haka sarkin Isra’ila ya tattara annabawa duka, mutane ɗari huɗu, ya kuma tambaye su, “Mu tafi yaƙi a kan Ramot Gileyad ko kada mu tafi?” Suka amsa “Tafi, gama Allah zai ba da shi cikin hannun sarki.”

6Amma Yehoshafat ya yi tambaya ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu tambaya?”

7Sarki Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, “Akwai guda har yanzu mai suna Mikahiya ɗan Imla, za mu iya nemi nufin Ubangiji daga gare shi, sai dai ba na sonsa domin bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni ba, sai kullum masifa.” Yehoshafat ya amsa ya ce, “Kada sarki yă faɗa haka.”

8Saboda haka sarkin Isra’ila ya kira ɗaya daga cikin ma’aikatansa ya ce, “A kawo Mikahiya ɗan Imla nan da nan.”

9Saye da rigunan sarakuna, sarki Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suna zaune a kan kujerunsu na mulki a masussuka ta ƙofar shigar Samariya, tare da dukan annabawa suna ta annabci a gabansu.

10To, fa, Zedekiya ɗan Kena’ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya kuma furta, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan za ka sassoki Arameyawa sai sun hallaka.’ ”

11Dukan sauran annabawan suka yi irin annabcin nan. Suka ce, “A haura zuwa Ramot Gileyad a yi nasara, gama Ubangiji zai ba da shi cikin hannun sarki.”

12Ɗan saƙon da ya tafi don yă kawo Mikahiya kuwa ya ce masa, “Duba, kowannen a cikin annabawa ya yi faɗin nasara wa sarki. Don haka kai ma ka yi maganar da za tă gamshi sarki kamar yadda suka yi.”

13Amma Mikahiya ya ce, “Na rantse da ran Ubangiji, zan faɗa masa kawai abin da Allahna ya faɗa.”

14Da suka iso, sarki ya tambaye shi, “Mika, mu tafi mu yaƙi Ramot Gileyad, ko kada mu tafi?” Ya amsa, “Kai masa yaƙi za ka kuwa yi nasara, gama za a ba da su a hannunka.”

15Sarki ya ce masa, “Sau nawa zan sa ka rantse don ka faɗa gaskiya a cikin sunan Ubangiji?”

16Sa’an nan Mikahiya ya amsa, “Na ga dukan Isra’ila sun warwatsu a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyaya, kuma Ubangiji ya ce, ‘Waɗannan mutane ba su da maigida. Bari kowanne yă tafi gida cikin salama.’ ”

17Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka cewa bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni, in ba masifa ba?”

18Mikahiya ya ci gaba, “Saboda haka sai ka ji maganar Ubangiji. Na ga Ubangiji yana zama a kan kursiyinsa tare da dukan rundunar sama tsaye a damansa da hagunsa.

19Ubangiji kuwa ya ce, ‘Wa zai ruɗe Ahab sarki Isra’ila zuwa yaƙi da Ramot Gileyad da kuma zuwa mutuwarsa a can?’ “Wani ya ba da wata shawara, wani kuma wata dabam.

20A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’ “ Ubangiji ya yi tambaya, ‘Ta wace hanya?’

21“Ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’ “ Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’

22“To yanzu, Ubangiji ya sa ruhun ruɗu a bakunan waɗannan annabawanka. Ubangiji ya ƙayyade masifa dominka.”

23Sai Zedekiya ɗan Kena’ana ya haura ya mari Mikahiya a fuska. Ya ce, “Ta wace hanya ce ruhun Ubangiji ya fita daga gare ni ya zo ya yi magana da kai?”

24Mikahiya ya amsa ya ce, “Za ka gane a ranar da ka je ka ɓuya a can cikin ɗaki.”

25Sa’an nan sarkin Isra’ila ya umarta, “Ɗauki Mikahiya ku aika da shi zuwa ga Amon mai mulkin birni da kuma ga Yowash ɗan sarki,

26ku ce ga abin da sarki ya ce, ‘Ku jefa wannan mutum a kurkuku kada kuma ku ba shi wani abu sai dai burodi da ruwa har sai na dawo lafiya.’ ”

27Mikahiya ya furta ya ce, “Idan har ka dawo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana ta wurina ba.” Ya kuma ƙara da cewa, “Dukanku mutane, ku lura da maganata!”

28Saboda haka sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suka haura zuwa Ramot Gileyad.

29Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Zan ɓad da kama in shiga yaƙin, amma ka sa kayanka na sarauta.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya ɓad da kama ya shiga cikin yaƙin.

30To, fa, sarkin Aram ya umarce shugabannin keken yaƙinsa ya ce, “Kada ku yaƙi kowa, ƙarami ko babba, sai dai sarkin Isra’ila.”

31Sa’ad da shugabannin kekunan yaƙi suka ga Yehoshafat, sai suka yi tsammani, “Wannan ne sarkin Isra’ila.” Saboda haka suka juya don su yaƙe shi, amma Yehoshafat ya yi ihu, Ubangiji kuma ya taimake shi. Allah ya janye su daga gare shi,

32gama sa’ad da shugabannin keken yaƙi suka ga cewa ba shi ne sarkin Isra’ila ba, sai suka daina binsa.

33Amma wani ya harba kibiya haka kawai, sai kibiyar ta sami sarki Ahab na Isra’ila a kafaɗa tsakanin rigar yaƙinsa na ƙarfe da ƙarfen ƙirjinsa. Sai sarki ya ce wa mai tuƙan keken yaƙi, “Juya ka fitar da ni daga wurin yaƙin. An ji mini rauni.”

34Duk yini yaƙi ya yi ta cin gaba, sarkin Isra’ila kuwa ya jingina kansa a cikin keken yaƙinsa yana duban Arameyawa har yamma. Sa’an nan a fāɗuwar rana sai ya mutu.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY