Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Koyarwa

Littattafan Bishara gefe da gefe · Koyarwa

Mai gini mai hikima da mai gini wawa

Mat 7:24–27 · Luk 6:46–49

Mattiyu

Mat 7:24–27

24“Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse.

25Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse.

26Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi.

27Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”

Luka

Luk 6:46–49

46“Don me kuke ce da ni, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ amma ba kwa yin abin da na faɗa?

47Zan nuna muku kwatancin mutumin da yakan zo wurina, yă ji kalmomina, yă kuma aikata.

48Yana kama da mutumin da ya gina gida, wanda ya haƙa ƙasa da zurfi, sa’an nan ya kafa tushen ginin a kan dutse. Da ambaliyar ruwa ta taso, ƙarfin ruwa kuwa ya buga gidan, wannan bai jijjiga shi ba, domin an yi masa tushen gini na ainihi.

49Amma wanda yakan ji kalmomina, ba ya kuma aikata su, yana kama da mutumin da ya gina gida a ƙasa, ba tare da ya kafa tushen gini ba. A sa’ad da ƙarfin ruwa ya buga gidan, sai gidan yă rushe, mummunar rushewa kuwa.”

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY