Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2027 › Disamba 24
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Disamba 24, 2027
Juma’a · Mako na 4 na lokacin Zuwan Ubangiji
Bukukuwa da waliyyai
24 ga Disamba
Ranar mako · Launin ibada: shunayya
Azumi da tuba
Ranar tuba
Kowace Juma’a ranar tuba ce; kowace taron bishop-bishop yana tsara yadda ake kiyaye ta: kamewa daga nama ko wani aikin tuba. Azumi ya wajaba daga shekara 18 zuwa 59, kamewa daga shekara 14.
Karatun yini
Karatu na farko
1Bayan sarki ya kama zama a fadansa Ubangiji kuma ya hutashe shi daga dukan abokan gābansa da suke kewaye da shi, 2sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar katakon al’ul, amma akwatin alkawarin Allah yana zaune a tenti.” 3Natan ya amsa wa sarki ya ce, “Duk abin da yake a zuciyarka, sai ka yi, gama Ubangiji yana tare da kai.” 4A daren nan maganar Ubangiji ta zo wa Natan cewa, 5“Je ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, kai ne za ka gina mini gida in zauna? 8“Yanzu, ka gaya wa bawana Dawuda ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauko ka daga makiyaya, daga kuma garken tumaki ka zama sarki bisan mutane Isra’ila. 9Na kasance tare da kai duk inda ka tafi, na kuma kawar da dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka yă shahara kamar sunayen shahararrun mutanen duniya. 10Zan kuma tanada wa mutanena Isra’ila wuri, in kuma dasa su yadda za su kasance da gida kansu ba tare da an ƙara damunsu ba. Mugayen mutane ba za su ƙara wahalshe su kamar dā ba, 11yadda suka yi tun lokacin da na naɗa shugabanni bisan mutanena Isra’ila, zan kuma hutashe ka daga hannun abokan gābanka. “ ‘ Ubangiji ya furta maka cewa Ubangiji kansa zai kafa maka gida. 12Sa’ad da kwanakinka suka ƙare, za ka huta tare da kakanninka, zan tā da zuriyarka, na cikinka, zan kuma sa mulkinsa ya kahu. 16Gidanka da kuma masarautarka za su dawwama har abada a gabana; gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.’ ”
Zaburar amsawa
1Maskil na Etan dangin Ezra. Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada; da bakina zan sanar da amincinka a dukan zamanai. 2Zan furta cewa ƙaunarka tana nan daram har abada, cewa ka kafa amincinka a sama kanta. 3Ka ce, “Na yi alkawari da zaɓaɓɓena, na rantse wa Dawuda bawana, 4cewa ‘Zan kafa zuriyarka har abada in kuma sa kursiyinka yă tsaya daram dukan zamanai.’ ” Sela 26Zai yi kira gare ni yă ce, ‘Kai ne Mahaifina, Allahna, Dutse mai cetona.’ 28Zan ci gaba da ƙaunarsa har abada, alkawarina da shi ba zai taɓa fasa ba.
Bishara
67Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci ya ce, 68“Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa. 69Ya tā mana ƙahon ceto a gidan bawansa Dawuda 70(yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki), 71cewa zai cece mu daga abokan gābanmu daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu 72don yă nuna jinƙai ga kakanninmu, yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki, 73rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim, 74don yă kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu, yă kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro, 75cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu. 76“Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki; gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya, 77don ka sanar da mutanensa ceto, ta wurin gafarar zunubansu, 78saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna, hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama, 79don yă haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu, da kuma cikin inuwar mutuwa, don yă bi da ƙafafunmu a hanyar salama.”
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi C, shekarar ranakun mako II.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi