Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2027 › Disamba 7

Kalandar Ortodoks · 24 ga Nuwamba (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Disamba 7, 2027

Talata · Mako na 25 bayan Fentekos · Sauti na 7

Bukukuwa da waliyyai

Afterfeast of the Entry of the Theotokos

Azumin Haihuwar Kiristi

Azumi: da mai

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Wasiƙa

2Tes 1:10–2:2

10a ranar da zai dawo don a ɗaukaka shi a cikin mutanensa masu tsarki, yă kuma zama abin banmamaki ga dukan waɗanda suka gaskata. Wannan ya haɗa har da ku, domin kun gaskata shaidar da muka yi muku. 11Sane da wannan, kullum muna addu’a saboda ku, don Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ta wurin ikonsa kuma yă cika kowace manufarku mai kyau da kuma kowane aikin da bangaskiyarku ta iza. 12Muna wannan addu’a don sunan Ubangijinmu Yesu yă sami ɗaukaka a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu da na Ubangiji Yesu Kiristi. 2:1Game da dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi da game da tattara mu gare shi, muna roƙonku, ’yan’uwa, 2kada ku yi saurin jijjiguwa ko kuwa hankalinku yă tashi ta wurin wani annabci, rahoto ko wasiƙar da an ce daga wurinmu ne, cewa ranar Ubangiji ta riga ta zo.

Bishara

Luk 17:26–37

26“Daidai kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a zamanin Ɗan Mutum. 27Mutane suna ci, suna sha, suna aurayya, ana kuma ba da su ga aure, har ranar da Nuhu ya shiga jirgin. Sa’an nan ambaliyar ruwan ya sauka, ya hallaka su duka. 28“Haka ma aka yi a zamanin Lot. Mutane suna ci, suna sha, suna saya, suna sayarwa, suna shuki, suna kuma gine-gine. 29Amma a ranar da Lot ya bar Sodom, sai aka yi ruwan wuta da farar wuta daga sama, aka hallaka su duka. 30“Daidai haka zai zama, a ranar da Ɗan Mutum zai bayyana. 31A ranan nan, kada wanda yake kan rufin gidansa ya sauka don yă kwashe dukiyarsa da take cikin gidan. Haka ma duk wanda yake gona, kada yă koma don wani abu. 32Ku tuna fa da matar Lot! 33Duk wanda yake so ya ceci ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai cece shi. 34Ina gaya muku, a daren nan, mutane biyu za su kasance a gado ɗaya, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan. 35Mata biyu za su kasance suna niƙan hatsi tare, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan.” 37Suka tambaya, suka ce, “A ina ne, ya Ubangiji?” Ya ce musu, “Ai, inda gawa take, nan ne ungulai za su taru.”

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Nuwamba 24 a kalandar ikilisiya shi ne Disamba 7 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi