Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Disamba 2026 › Disamba 23

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Disamba 23, 2026

Laraba · Mako na 4 na lokacin Zuwan Ubangiji

Bukukuwa da waliyyai

23 ga Disamba

Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: shunayya

Waliyyi John na Kanty, firist · Ambato

Karatun yini

Karatu na farko

Mal 3:1–4; 4:5–6

1“Duba, zan aika manzona, wanda zai shirya hanya a gabana. Sa’an nan a farat ɗaya Ubangiji wanda kuke nema zai zo haikalinsa. Manzon alkawari, wanda kuke sa zuciya kuwa zai zo,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. 2Amma wa zai jure wa ranar zuwansa? Wa zai iya tsaya sa’ad da ya bayyana? Gama zai zama kamar wuta mai tace ƙarfe, ko sabulu mai wanki. 3Zai zama kamar mai tace azurfa da mai tsarkaketa; zai tsabtacce Lawiyawa, yă kuma tace su kamar zinariya da azurfa. Sa’an nan Ubangiji zai sami mutanen da za su kawo hadayu a cikin adalci. 4Hadayun Yahuda da na Urushalima za su zama yardajje ga Ubangiji, za su zama kamar a kwanakin da suka wuce, kamar a shekarun baya. 4:5“Ga shi, zan aika muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji tă zo. 6Zai juye zukatan iyaye ga ’ya’yansu, zukatan ’ya’ya kuma ga iyayensu; in ba haka ba zan bugi ƙasar da hallaka gaba ɗaya.”

Zaburar amsawa

Zab 25:4–5, 8–10, 14

4Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji, ka koya mini hanyoyinka; 5ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini, gama kai ne Allah Mai cetona, kuma begena yana a kanka dukan yini. 8Ubangiji nagari da mai adalci ne; saboda haka yakan koyar da masu zunubi a hanyoyinsa. 9Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai ya kuma koyar da su hanyoyinsa. 10Dukan hanyoyin Ubangiji ƙaunatattu ne da kuma aminci ga waɗanda suke kiyaye abin da alkawari ya bukaci. 14Ubangiji yakan amince da waɗanda suke tsoronsa; yakan sa su san alkawarinsa.

Bishara

Luk 1:57–66

57Sa’ad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa. 58Maƙwabtanta da ’yan’uwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki. 59A rana ta takwas, sai suka zo don a yi wa yaron kaciya, dā za su sa masa sunan mahaifinsa Zakariya ne, 60amma mahaifiyar yaron ta ce, “A’a! Za a ce da shi Yohanna.” 61Sai suka ce mata, “Ba wani a cikin danginku mai wannan suna.” 62Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron. 63Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna.” Dukan mutane kuwa suka yi mamaki. 64Nan da nan bakinsa ya buɗe harshensa kuma ya saku, sai ya fara magana yana yabon Allah. 65Maƙwabta duk suka cika da tsoro, mutane kuwa suka yi ta yin magana game da dukan waɗannan abubuwa a ko’ina a cikin ƙasar tudu ta Yahudiya. 66Duk waɗanda suka ji wannan kuwa sun yi mamaki suna cewa, “To, me yaron nan zai zama?” Gama hannun Ubangiji yana tare da shi.

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi